Super Falcons ta gayyaci 'yan wasan da za ta fuskanci Habasha

Super Falcons

Asalin hoton, Super Falcons Twitter

An wallafa

Tawagar Najeriya ta mata, Super Falcons ta gayyaci 'yan wasan da za su buga mata karawar neman gurbin shiga Olympic da za a yi a Paris a 2024.

A cikin watan Oktoba Najeriya za ta fafata da Habasha gida da waje a fafatawar kwallon kafar mata don fitar da wadda za ta wakilci Afirka.

Cikin 'yan wasa 22 da aka gayyata har da mai tsaron raga Chiamaka Nnadozie da mai tsaron baya, Osinachi Ohale da mai cin kwallaye, Asisat Oshoala.

Habasha ce za ta fara karbar bakuncin karawar farko a Adfis Ababa ranar Laraba 25 ga watan Oktoba, yayin da a kara a wasa na biyu ranar Talata 31 ga watan nan a Najeriya.

Habasha ce ta fitar da Chad a wasan zagayen farko a neman gurbin shiga Olympic, inda Najeriya ta dauki hutu.

Super Falcons ce ta kare a mataki na takwas daga kasashe 332 da suka buga gasar kofin duniya da aka a Austalia da New Zealand.

Haka kuma Najeriya ta dauko hutu a zangon zagaye na uku a neman shiga gasar kofin nahiyar Afirka da za a yi a 2024.

Kenan Falcons din za ta kece raini da tawagar Cape Verde a karshen watan Nuwamba a wasannin neman shiga gasar cin kofin Afirka.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Birnin Paris din Faransa zai karbi bakuncin wasannin Olympic a 2024. Falcons din ta halarci Olympic a 2000 da 2004 da kuma 2008.

'Yan wasan Super Falcons da aka gayyata:

Masu tsaron raga: Chiamaka Nnadozie (Paris FC); Tochukwu Oluehi (Shualat Alsharqia FC, Saudi Arabia); Monle Oyono (Bayelsa Queens)

Masu tsaron baya: Osinachi Ohale (Pachuca FC, Mexico); Comfort Folorunsho (Edo Queens); Oluwatosin Demehin (Stade de Reims, France); Michelle Alozie (Houston Dash, USA); Nicole Payne (Paris Saint Germain, France); Jumoke Alani (Edo Queens); Rofiat Imuran (Stade de Reims, France)

Masu buga tsakiya: Halimatu Ayinde (Rosengard FC, Sweden); Peace Efih (Sporting Club de Braga, Portugal); Christy Ucheibe (SL Benfica, Portugal); Rasheedat Ajibade (Atletico Madrid FC, Spain); Toni Payne (Sevilla FC, Spain); Regina Otu (AS Saint Etienne, France)

Masu cin kwallaye: Omorinsola Babajide (Coasta Adeje Tenerife Egatesa, Spain); Ifeoma Onumonu (NY/NJ Gotham FC, USA); Asisat Oshoala (FC Barcelona Feminine, Spain); Uchenna Kanu (Racing Louisville, USA); Gift Monday ((Coasta Adeje Tenerife Egatesa, Spain); Opeyemi Ajakaye (FC Robo Queens)