Arsenal ta taya Bakayako, Tottenham na son Eze, Rabiot zai koma Man United

An wallafa

Tottenham ta shirya tsaf domin siyan Eberechi Eze, Brighton na zawarcin Kiernan Dewsbury-Hall, yayin da Arsenal ke neman Johan Bakayoko.

Tottenham na sha'awar dauko dan wasan gaban Crystal Palace Eberechi Eze, mai shekara 25 (Talksport)

Brighton na son dauko dan wasan Leicester dan kasar Ingila Kiernan Dewsbury-Hall, mai shekara 25. (Telegraph)

Arsenal ta nemi sayen dan wasan gaban PSV Eindhoven dan kasar Belgium Johan Bakayoko, mai shekara 21. (DHNet)

Bayern Munich ta ci gaba da zawarcin dan wasan tsakiya na Portugal Joao Palhinha, mai shekara 28, amma ba za ta iya biyan fam miliyan 60 da Fulham ke nema ba. (Telegraph)

Aston Villa na tunanin zawarcin dan wasan gefe na Sporting Lisbon Pedro Goncalves, mai shekara 25. (A Bola)

Ipswich na tattaunawa da dan wasan baya na Ingila Ben Johnson, mai shekara 24, don daukarsa a kyauta, lokacin da kwantiraginsa da West Ham zai kare a mako mai zuwa. (East Anglian Daily Times)

Manchester United ta tattauna da Juventus kan sayen Adrien Rabiot, amma tana fuskantar hamayya daga Arsenal da Aston Villa kan dan wasan tsakiyar na Faransa mai shekara 29. (Teamtalk)

Nottingham Forest da Brighton na zawarcin dan wasan kungiyar Sogndal ta Noway, dan asalin Ghana Edmund Baidoo mai shekara 18, . (Sky Sports)

Kocin Manchester United Erik ten Hag na shirin kulla sabuwar yarjejeniya da kungiyar. (Fabrizio Romano)

Barcelona za ta iya nuna sha'awar aron dan wasan Ingila Jadon Sancho mai shekaru 24 bayan tattaunawa da Manchester United. (Sports Spanish)

Dan wasan Leeds dan kasar Sipaniya Marc Roca, mai shekara 27, yana tattaunawa da Real Betis kan yarjejeniyar dindindin bayan ya kulla yarjejeniya da kungiyar a matsayin aro a kakar wasan da ta wuce. (Football Insider)

West Ham ta shirya barin dan wasan Ingila Danny Ings, mai shekara 31, ya bar kungiyar a bazara kuma Southampton ta nuna sha'awar daukarsa. (Football Insider)

An ba wa Barcelona aron dan wasan Hull dan kasar Ingila, Jaden Philogene, mai shekara 22. Daga baya kungiyar na da damar sayansa. (Sports Spanish)