Real za ta nemi a rage hukuncin da aka yi wa Bellingham a La Liga

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Carlo Ancelotti ya ce Real Madrid za ta ɗaukaka kara, domin a rage yawan wasan da Jude Bellingham ba zai yi ba a La Liga.

An bai wa ɗan wasan tawagar Ingila jan kati a wasan da Real Madrid ta je ta tashi 1-1 da Osasuna.

Hakan ya biyo bayan da rafli, ya rubuta a rahotonsa da aka tashi daga karawar cewar Bellingham ya faɗa masa kalaman da ba su dace ba.

Daga nan hukumar ƙwallon kafa ta Sifaniya ta dakatar da shi wasa biyu, shi ne wanda Real za ta yi da Girona ranar Lahadi da wanda za ta yi da Real Betis ranar 2 ga watan Maris.

Haka kuma Belligham ba zai yi Real wasan farko a zagayen ƴan 16 da Atletico Madrid ba, saboda ya karɓi katin gargaɗi uku a Champions League.

Tun farko hukumar ƙwallon kafa ta Sifaniya ta yi watsi da ɗaukaka karar da Real ta shigar na a soke jan katin, yanzu tana son a rage yawan wasan da ba zai yi ba.

Real Madrid wadda za ta karɓi bakuncin Girona ranar Lahadi a Santiago Bernabeu tana ta biyu a teburin La Liga da maki 51 iri ɗaya da na Barcelona ta biyu.

Barcelona za ta je gidan Las Palmers ranar Asabar a gasar ta La Liga.

Ancelooti ya sanar da cewar Dani Ceballos yana cikin koshin lafiya, bayan da Real ke fama da masu tasre baya da ke jinya.