Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
An karbe ragamar Bundesliga a hannun Bayern Munich
Bayan Munich ta yi rashin nasara a hannun Bayern Leverkusen da ci 2-1 an karbe ragamar teburin Bundesliga a wajenta.
Ranar Lahadi suka buga wasan mako na 25, inda Bayern Munich, wadda ta kai ziyara ta fara cin kwallo a minti na 22 ta hannun Joshua Kimmich.
Bayan da suka koma zagaye na biyi ne Leverkusen ta farke biyun ta hannun Exequiel Palacios, kuma dukkansu a bugun fenariti.
Da wannan sakamakon Bayern ta koma ta biyu a teburin Bundesliga da tazarar maki daya tsakaninta da Borussia Dortmund, wadda ta koma ta daya.
Dortmund, wadda ta caskara Kohl 6-1 ranar Asabar a Bundesliga ta hau kan teburin Jamus a karon farko tun bayan 2019.
Leverkusen, wadda Xabi Alonso ke horar da ita, wanda ya taba yin Bayern, ya ci wasa biyar a jere a dukkan fafatawa.
Dortmund da Bayern za su kara a tsakaninsu a karon farko a bana ranar 1 ga watan Afirilu a gasar Bundesliga.