Arsenal da Chelsea na gogayya kan Isak, United na zawarcin Davies

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 2

Arsenal da Chelsea suna farautar ɗan wasan gaba kuma ƙungiyoyin na Landan suna da jerin sunayen da ya ƙunshi sunan ɗan wasan Newcastle United da Sweden Alexander Isak mai shekara 25. (Caught Offside)

Manchester United ma na cikin ƙungiyoyi masu neman ɗan wasan gaba kuma za ta matsa ƙaimi wurin yin hakan a watan Junairu. (Mirror)

Bayern Munich ta yi gagarumin ci gaba game da batun tsawaita kwantiragin ɗan ƙasar Canada Alphonso Davies, inda Manchester United ke sane da cewa ɗan wasan mai shekara 24 zai iya rattaba hannu kan wata sabuwar yarjejeniya duk da sha'awar da ta nuna a kansa. (Sky Germany)

Manchester United na fafatawa da Chelsea a fafatukar neman ɗan wasan Lecce ɗan ƙasar Denmark Patrick Dorgu mai shekaru 20. (Teamtalk)

Wolves da West Ham sun tattauna da tsohon kocin Chelsea da Brighton Graham Potter. (Talksport)

Tsohon kocin Borussia Dourtmund Edin Terzic ba zai zama sabon kocin West Ham ba idan aka kori Lopetegui daga mukaminsa, amma tsohon kociyan Denmark Kasper Hjulmand na cikin ƴan takarar zama kocin kulob ɗin. (Florian Plettenberg)

Tsohon kocin West Ham David Moyes na daga cikin waɗanda ke iya karɓar ragamar Wolves idan aka sallami Gary O'Neil amma kocin Luton Rob Edwards na cikin ƴan takara sakamakon zaman shekaru huɗu da ya yi a Molineux a matsayin ɗan wasa. (Telegraph)

Liverpool ta tuntuɓi Bayer Leverkusen kan yiwuwar ɗaukar ɗan wasan baya na ƙasar Holland Jeremie Frimpong, mai shekara 23. (Caught Offside)

Daraktan ƙwallon ƙafa na Barcelona Deco ya gana da wakilan ɗan wasan baya na Jamus Jonathan Tah, mai shekara 28, wanda kwantiraginsa zai ƙare a Bayer Leverkusen a bazara mai zuwa. (Mundo Deportivo)

Manchester City za ta bar ɗan wasan Belgium Kevin De Bruyne, mai shekara 33, ya koma ɗaya daga cikin ƙungiyoyin da ke kawance da ita idan ya bar ƙungiyar ta Premier. (Telegraph)

Amma ƙungiyar Inter Miami ta David Beckham ta mayar da De Bruyne babban kan gaba a jerin ƴan wasan da ta ke zawarci. (Mirror)

Roma na zawarcin ɗan wasan gaban Everton da Guinea-Bissau Beto, mai shekara 26, da ɗan wasan Mali Abdoulaye Doucoure, mai shekara 31. (Gazzetta dello Sport)