Bayan Messi da Ronaldo – sabbin matasan da ke haskawa a gasar cin kofin duniya

Asalin hoton, Getty Images
Ba wai kawai fitattun taurari a fannin taka leda wato Lionel Messi da Cristiano Ronaldo kaɗai suke yin fice a gasar cin kofin duniya ta 2026 – akwai sabbin matasa masu tasowa da suma suke taka rawar gani.
Daga cikin ƴan wasa 85 masu shekara 21 ko ƙasa da haka da suke wakiltar tawagoginsu a gasar da ake gudanarwa a Amurka da Mexico da kuma Canada da dama suna yin anfani da wannan damar da suka samu, kuma suna taka leda ba tare da tsoro ba.
Ɗan wasan Senegal, Ibrahim Mbaye, mai shekara 18 da kwanaki 143, ya zama matashin ɗan wasa na huɗu mafi ƙarancin shekaru da ya zura ƙwallo a raga a tarihin Gasar Cin Kofin Duniya, wanda ya ci ɗaya a wasan da Senegal ta yi rashin nasara 3-1 a hannun Faransa a karawar cikin rukuni a New Jersey ranar 16 ga watan Yuni.
Kwana biyar bayan haka, Lamine Yamal (mai shekara 18 da kwana 343) ya ci ƙwallon farko a karawar da Sifaniya ta doke Saudiyya 4-0 a Atlanta.
Sauran matasan ƴan wasa kuwa suna yin fice da nuna bajinta da ƙwazo ba tare da kafafen yaɗa labarai sun fuskanci irin rawar da suke takawa ba, saboda yanzu ne suke son nuna kansu a fannin taka leda.
Matashin ɗan wasan tawagar Mexico, Gilberto Mora, ma ba a ma haife shi ba a lokacin da Messi da Ronaldo da kuma Luka Modric suka buga Gasar Cin Kofin Duniya ta shekarar 2006.
Mora ya zama mafi ƙarancin shekaru da ya wakilci ƙasar da ke karɓar bakuncin gasar bana mai shekara 17 da kwana 240, wanda ya fara daga benci ya kuma yi canji a wasan da Mexico ta doke Afirka ta Kudu da ci 2-0, wanda shi ne wasan farko na buɗe gasar nan a ranar 11 ga watan Yuni.
Tun da farko man yi hasashen cewa Lamine Yamal zai kasance ɗaya daga cikin manyan ƴan wasan da za su haska a wannan Kofin Duniya.
Amma su waye matasa taurarin da suka fito suka nuna kansa daga matakin rukuni?
BBC Sport ta yi nazari kan matasa biyar da suka ɗauki hankali da bajintarsu a gasar.
Ayyoub Bouaddi (Morocco shekara 18)

Asalin hoton, Getty Images
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
A wasansa na farko a Gasar Cin Kofin Duniya da Brazil ranar 13 ga watan Yuni, ɗan wasan da ke taka leda a Lille, Ayyoub Bouaddi, ya zama na biyu mafi ƙarancin shekaru a wannan ƙarni da ya raba ƙwallo fiye da sau 50 a wasa ɗaya a gasar Kofin Duniya, jimilla 66 ya yi, wanda ya yi bajinta mai jan hankali.
Tsohon ƙyaftin ɗin Ingila, Alan Shearer, wanda ke sharhi kan wasan ga BBC Sport, ya yaba wa matashin ɗan wasan, yana cewa:
"Bouaddi ya nuna natsuwa sosai da ƙwallo mai ban sha'awa, kuma ya yi ƙoƙarin jagorantar yadda wasa ke gudana a tsakiyar fili."
Daga baya, matashin ya ƙara kafa wani tarihi inda ya zama ɗan wasa na farko mai shekara 18 ko ƙasa da haka tun daga shekarar 1966 da ya yi wasa biyu da ya raba ƙwallo 50 ko fiye da haka a kowannensu.
Wannan bajinta ta nuna cewa Bouaddi na daga cikin fitattun matasan 'ƴan wasan da ke haskakawa a Gasar Cin Kofin Duniya ta 2026, kuma yana da kyakkyawar makoma a harkar ƙwallon ƙafa a duniya.
Yan Diomande (Ivory Coast shekara 19)

Asalin hoton, Getty Images
Paris Saint-Germain (PSG) ta nuna sha'awar sayen ɗan wasan, Yan Diomande. Haka kuma Liverpool na cikin ƙungiyoyin da ke neman sa.
Ba abin mamaki ba ne idan aka yi la'akari da irin bajintar da wannan matashin ɗan wasan na RB Leipzig ke nunawa a Gasar Cin Kofin Duniya ta bana, musamman wajen wuce abokan hamayya da gudu da ƙwallo.
A wasan da Ivory Coast ta doke Ecuador da ci 1-0, Diomande ya samar da damar cin ƙwallo guda biyar ga abokan wasansa. Daga baya kuma ya bayar da ƙwallo masu kai da nufin a karasa zurasu a raga masu haɗari a wasan da suka sha kashi 2-1 a hannun Jamus.
Tsohon kocin Tottenham da Brentford, Thomas Frank, ya yaba masa sosai a hirarsa da BBC Sport, yana cewa:
"Diomande shi ne wanda kowa ke magana a kai a halin yanzu. Abubuwan da zai iya yi da ƙwallo suna cikin ƙwaƙwalwata sosai."
A baya, Ivory Coast ta kasa tsallakewa daga matakin rukuni a dukkan fitowarta uku na baya a Gasar Cin Kofin Duniya.
Sai dai Diomande na ɗaya daga cikin manyan dalilan da suka sa ƙasar ta samu nasarar kaiwa zagaye na biyu a karon farko a tarihinta. Bajintarsa da kuzarin da yake nunawa sun sa ya zama ɗaya daga cikin fitattun matasan taurarin da ke haskakawa a gasar.
Johan Manzambi (Switzerland 20)
Johan Manzambi ya fara da tsaron raga a lokacin da yake matashi - kuma gwaninsa shi ne golan tawagar Jamus, Manuel Neuer.
Sai dai yanzu yana taka leda daga gurbin tsakiya, wanda yake jin daɗin jan ƙwallo zuwa gidan abokan hamayya da zura ƙwallaye a raga.
Ƙwallo uku daga bakwai da tawagar Switzerland ta zura a raga a karawar cikin rukuni Manzambi ne ya ci, wanda yake da shekara 20 da kwana 247 - wanda ya zama matashi na farko a tarihin gasar cin kofin duniya da ya ci ƙwallo biyu ko fiye da haka, bayan da ya shiga wasa daga baya ya yi canji - kuma shi ne mai wannan bajinta a Switzerland a babbar gasar tamaula ta duniya.
Hakan ya faru ne a karawa da Bosnia-Herzegovina ranar 18 ga watan Yuni. ya shiga fili a lokacin da Switzerland ke cin ƙwallo a minti na 71 a fafatawar da kasar ta yi nasarar 4-1.
Manzambi yana cikin matasa uku da suke da kasa da shekara 21 da suke da hannu a cin ƙwallo huɗu - ya zura uku a raga ya bayar da ɗaya aka ci a gasar cin kofin duniya, bayan tarihin da Kylian Mbappe ya kafa na sa hannu a cin ƙwallo huɗu a 2018 da kuma a 2010 da Thomas Muller keda hannu a cin ƙwallo takwas a 2010.
Kerim Alajbegovic (Bosnia-Herzegovina, shekara 18)
Kerim Alajbegovic, mai shekaru 18 da kwana 276, ya zama ɗan wasa mafi ƙarancin shekaru da aka taɓa samu (tun daga shekarar 1966) da ya ci ƙwallo daga wajen yankin bugun fenariti a Gasar Cin Kofin Duniya. Ya kafa wannan tarihi ne lokacin da ya fara ciwa Bosnia da Herzegovina kwallon a wasan da ta yi da Qatar ranar 24 ga watan Yuni.
Da wannan, ya doke tarihin da Kylian Mbappe ya kafa a wasan da Faransa ta buga da Croatia a shekarar 2018, lokacin da Mbappe ya ci wata ƙwallo mai ban sha'awa daga wajen da'ira ta 16, yana da shekaru 19 da kwanaki 207.
Matashin ɗan wasan, wanda ya buga wa Red Bull Salzburg tamaula a kakar da ta gabata, ya taka leda a dukkan wasannin rukuni uku na Bosnia da Herzegovina, inda ya fara wasa biyu daga cikinsu, yayin da ƙasar ta tsallake zuwa matakin na gaba.
Yanzu Bosnia da Herzegovina za ta kara da ɗaya daga cikin ƙasashen da ke ɗaukar nauyin gasar, wato Amurka, a jihar California ranar 1 ga watan Yuli.
A nasarar da Bosnia da Herzegovina ta samu da ci 3-1 a kan Qatar, Alajbegovic ya kasance fitaccen ɗan wasa a fagen tamaula. Ya:
Nestory Irankunda (Australia, shekara 20)
Nestory Irankunda mai shekara 20 da kwana 125, ya zama mafi ƙarancin shekaru da ya taba zura ƙwallo a tawagar Australia a Gasar Cin Kofin Duniya lokacin da ya fara zura ta farko a ragar Turkiyya a karawar da suka yi nasarar cin 2-0.
Haka kuma, ya zama ɗan wasa na huɗu da ya zura ƙwallo a wasansa na farko a Gasar Cin Kofin Duniya ga Australia, bayan John Aloisi da Tim Cahill da kuma Craig Goodwin.
Da yake magana bayan wasan, Irankunda ya ce:
"Abu ne mai ban mamaki kuma mafarki na ya cika a gare ni."
An haifi Irankunda ne a shekarar 2006 a wani sansanin ƴan gudun hijira da ke Tanzania, Iƴayensa ƴan ƙasar Burundi waɗanda suka tsere daga ƙasarsu saboda yaƙin basasa.
Magoya bayan ƙungiyar Watford sun riga sun san irin ƙwarewarsa, domin ya zura ƙwallaye huɗu a kakar gasar Championship ta 2025-26.
Ya koma Watford ne daga Bayern Munich a shekarar 2025, inda ake saka shi a wasanni koda yaushe, kuma rawar da yake takawa ta sa kasar ta gayyace shi a karon farko.











