Batutuwa kan wasan Barcelona da Real Madrid a La Liga

Asalin hoton, Getty Images
Barcelona da Real Madrid za su kece raini ranar Lahadi a La Liga wasan hamayya da ake kira El Clasico, kuma karo na huɗu da za su fuskanci juna a bana.
Real Madrid na bukatar cin wasan, domin samun damar ɗaukar La Liga, saboda ta yi ban kwana da Carlo Ancelotti tare da kofin da take riƙe da shi.
Sai dai Barcelona na fatan wannan shi ne El Clasico na karshe da za ta yi a filin Olympic - yayin da za a buɗe Nou Camp a kakar baɗi.
BBC ta duba batuwan da suka shafi wasan na El Clasico.

Asalin hoton, BBC Sport
Barcelona ce ta ɗaya a teburin La Liga da tazarar maki huɗu tsakani da Real Madrid, kuma saura wasa hurhuɗu a karkare kakar nan.
Idan Barcelona ta yi nasara a kan Real Madrid zai koma tazarar maki bakwai tsakaninsu, idan Real ce ta ci karawar, zai zama saura maki ɗaya a tsakani.
Wasa biyu daga ukun da Barcelona za ta buga nan gaba da ƙungiyoyin da ke gurbin Champions League ne a teburin La Liga, wato za ta fafata a gida da Villarreal da zuwa gidan Athletic Bilbao.
Ita kuwa Real Madrid daga cikin wasan da zai rage mata, Mallorca ce kaɗai da za ta yi tata ɓurza daga ciki, wadda take ta 10 a teburin babbar gasar tamaula ta Sifaniya.
A kakar nan ta bana, Barcelona ta ci ƙwallaye 91 a La Liga, yayin da Real Madrid ta zura 69 a raga.
Ko wannan ne El Clasico na karshe ga Ancelotti?
Watakila wannan shi ne wasan karshe da Carlo Ancelotti zai ja ragamar El Clasico.
Ɗan kasar Italiya, mai shekara 65 ya fara horar da Real Madrid daga 2013 zuwa 2015, sannan ya karɓi aikin a karo na biyu daga 2021.
Ancelotti shi ne na farko da ya ja ragamar Real Madrid ta lashe kofi 15 - har da Champions League uku da La Liga biyu.
Wannan ce dama ta karshe da zai ɗauki kofi na 16 jimilla a Real Madrid.
Babu wata sanarwa da aka fitar kan makomar Ancelotti a Real Madrid, amma ana sa ran zai ajiye aikin a karshen kakar nan, watakila kafin gasar Fifa Club World Cup da za a fara daga watan Yuni a Amurka.
Ana kuma sa ran tsohon ɗan wasan Liverpool da Real Madrid, Xabi Alonso, wanda ya taka rawar gani a Bayer Leverkusen, shi ne zai maye gurbin Ancelotti.
Ko Flick zai yi nasara huɗu a El Clasico a kaka ɗaya?
Hansi Flick na taka rawar gani a kakar farko a Barcelona - ya lashe kofi biyu a kan Real Madrid a wasan na hamayya na El Clasico.
Watakila kociyan ɗan kasar Jamus ya doke Real Madrid karo na huɗu a bana a wasan na El Clasico da za su yi ranar Lahadi.
Barcelona ta ɗura 4-0 a ragar Real Madrid a Santiago Bernabeu cikin watan Oktoban 2024, karon farko a bana da suka fafata a gasa kenan.
Sun kara fuskantar juna a cikin watan Janairu a Saudiyya, inda Barcelona ta lashe Spanish Super Cup da cin 5-2, duk da an kori mai tsaron ragar Barca, Wojciech Szczesny a minti na 56.
A cikin watan Afirilu, Barcelona ta yi nasarar cin Real Madrid 3-2 har da karin lokaci, hakan ya sa ta lashe Copa del Rey a kakar nan.
Wa zai haska tsakanin Yamal ko Mbappe?

Asalin hoton, Getty Images
Ana ta magana kan rawar da Lamine Yamal ke takawa a kakar nan - musamman a Champions League da suka kai daf da karshe, inda Inter Milan ta fitar da Barcelona.
Matashin ɗan wasan mai shekara 17 ya bayar da ƙwallo 21 aka zura a raga a dukkan fafatawa, shi kuma da kansa ya ci 14.
Cikin karawar ta EL Clasico a bana, Yamal ya ci ƙwallo biyu ya bayar da biyu aka zura a raga kawo yanzu.
Kylian Mbappe, wanda lokacin da yake da shekara 17, shima an yi ta batunsa, yanzu yana taka rawar gani a kakar farko a Real Madrid.
Ƙyaftin ɗin tawagar Faransa, mai shekara 26 ya ci ƙwallo 35 a dukkan fafatawa a Real Madrid a kakar nan.
A jerin masu cin ƙwallaye a La Liga a kakar nan yana mataki na biyu da 24 a raga, bayan da Robert Lewandowski na Barcelona ke matakin farko mai 25.
Ko Bellingham zai dawo da martabarsa a Clasico?
A kakarsa ta farko a bara a Real Madrid, ɗan wasan tawagar Ingila, Jude Bellingham shi ne sarki a wasan hamayya na El Clasico.
Real ce ta yi nasara uku daga fafatawa ukun da suka yi bara -- ciki har da lashe Spanish Super Cup a kan Barca, sannan Bellingham ne ya zama gwarzo a La Liga gida da waje a baran.
A cikin watan Oktoba, Bellingham ya farke ƙwallo daga yadi na 30, sannan ya ci na biyu a karawar da Real Madrid ta ci Barcelona 2-1.
A cikin watan Afirilu, shi ne ya zura na uku a raga da Real ta yi nasarar cin Barca 3-2 a Santiago Bernabeu.
A kakar nan Bellingham yana kan ganiya, wanda ya ci ƙwallo 13 a raga - sai dai bai zura ƙwallo a ragar Barcelona ba a bana.
Ko wannan wasan zai samu zura cin Barcelona a wasan na hamayya na El Clasico?
Waɗan da ke kan gaba a yawan cin ƙwallaye:
- Lewandowski Barcelona 25
- Mbappé R. Madrid 24
- Budimir Osasuna 18
- Raphinha Barcelona 16
- Pérez Villarreal 16
- Sancet A. Club 15
- Alvarez Atletico 15
- Sørloth Atletico 13
- García D. Alaves 12
- Júnior R. Madrid 11










