Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Liverpool za ta gwada lafiyar Wirtz, United ta shirya wa Osimhen
Florian Wirtz ya shirya tsaf a tantance lafiyarsa a Liverpool bayan da suka cimma yarjejeniya da Bayer Lerverkusen don ɗaukan ɗanwasan tsakiyar na Jamus mai shekara 22 a kan kuɗi fam miliyan 127. (Fabrizio Romano)
Arsenal ta amince ta biya kusan fam miliyan 59 domin sayen ɗanwasan Real Sociedad Martin Zubimendi mai shekara 26 inda za a kammala sayen shi bayan 1 ga watan Yuli don cika ƙa'idojin taƙaita kashe kuɗi. (AS - in Spanish)
Manchester United na tantance tayi kan ɗanwasan Napoli mai bugawa Najeriya Victor Osimhen mai shekara 26 ta hanyar cefanar da ɗanwasan gaban Netherlands Joshua Zirkzee mai shekara 24 a wani ɓangare na yarjejeniyar. (Gazzetta dello Sport - in Italian)
Ɗanwasan RB Leipzig mai shekara 22 Benjamin Sesko - wanda rahotanni ke cewa Arsenal na ƙyalla ido kan shi - ya yi watsi da batun koma wa ƙungiyar Al-Hilal ta Saudiyya kafin cikar wa'adin kasuwar musayar ƴanwasa a ranar Talata. (Star)
Ɗanwasan Hungary Milos Kerkez mai shekara 21, na gab da koma wa Liverpool kan fam miliyan 45 bayan da Bournemouth ta amince da yarjejeniyar ɗaukan ɗanwasan Faransa Adrien Truffert mai shekara 23 daga Rennes. (Telegraph - subscription required)
Newscastle United ta buɗe babin tattaunawa da Burnley kan ɗaukan gola James Trafford mai shekara 22. (Times - subscription required)
Gianluigi Donnarumma na son ci gaba da zama a Paris St-Germain duk da cewa Manchester United da Inter Milan na neman ƙarin haske kan golan na Italiya mai shekara 26. (ESPN)
Brighton za ta karɓi tayin fam miliyan 50 zuwa miliyan 60 kan ɗanwasan Brazil mai shekara 23, Joao Pedro, wanda kuma Newcastle ke zawarci. (Football Insider)
Ƙofar Chelsea a buɗe take domin karɓar tayi kan ɗanwasa Benoit Badiashille, mai shekara 24 da kuma Axel Disasi mai shekara 27. (Football Insider)
Inter Milan ta ƙagu ta sayi ɗanwasan tsakiya na Paraguay Julio Enciso daga Brighton a wannan bazara. (Teamtalk)
Yunƙurin Al-Hilal na ɗaukan ɗanwasan tsakiyar Faransa N'Golo Kanye mai shekara 34, na ɗan gajeran lokaci daga ƙungiyar Al-Ittihad ita ma a Saudiyya don buga gasar Club World Cup na iya wargajewa saboda sukar da wani magoyin baya ya yi. (Talksport)