Dalilin da Barca ta bukaci Gundogan ya koma wata ƙungiyar

Gundogan

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Barcelona ta sanar ta cewar Ilkay Gundogan zai iya barin ƙungiyara a bana, domin ya gwada sa'a idan damar ta samu.

Gundogan ya taka rawar gani a ƙungiyar a kaka ɗaya da ya buga, bayan da ya koma Sifaniya daga Manchester City, to amma Barcelona na fama da matsin tattalin arziki.

A farkon makon nan Barcelona ta sanar da ɗaukar Dani Olmo daga RB Leipzig, amma bai buga mata wasan da ta je ta ci Valencia ba a La Liga ranar Asabar.

Haka shima Gundogan bai buga wa Barcelona karawar da ta fara da haɗa maki uku ba a bana, sai dai koci, Hansi Flick ya ce ɗan wasan yana jinya.

Wasu na cewar har yanzu Barcelona ba ta kammala biyan kuɗn Olmo ba, watakila shi ya sa ba ta saka shi a wasan da ta ci 2-1 ba a makon farko a La Liga.

Gasar La Liga ta fayyace cewa ƙungiya ta kashe kuɗi daidai samu a duk kakar tamaula, inda Barcelona ta haura ka'ida, wadda take ta kokarin bin dokar.

Saboda haka dole sai Barcelona ta nemi kuɗi daga ciki har da sayar da ƴan wasa ko hakura da wasu masu ɗaukar albashi mai tsoka, kafin ta kammala cinikin Olmo.

Gundogan yana daga cikin ƴan wasan Barcelona da ke karɓar albashi mai yawa, bayan da ya koma ƙungiyar daga Manchester City, yana da sauran ƙunshin yarjejeniya.

Kenan Barcelona za ta iya sayar da ɗan ƙwallon Jamus, koda ba a taya da tsada ba, domin ta rage yawan albashin da take biyansa.