Yaƙin Tigray: 'Na kasa tura kuɗi ga dangina da ke cikin tsananin yunwa'

An wallafa

Shugaban Hukumar Lafiya ta Duniya Dakta Tedros Ghebreyesus, ya bayyana cewa ya kasa aika wa da kuɗi ga ƴan uwansa waɗanda ke fama da tsananin yunwa a yankin Tigray na Habasha da yaƙi ya ɗaiɗaita.

"Ina da dangi da yawa a can. Ina so na aika musu da tallafi. Ba zan iya tura musu kuɗi ba," kamar yadda ya bayyana a wani taron manema labarai.

"Ban san wanda ya mutu ba ko wanda ke raye," in ji shi.

Ko a ranar Juma'a sai da hari ta sama ya yi sanadin mutuwar mutum huɗu, ciki har da yara, kamar yadda wani ma'aikacin lafiya ya bayyana.

Tun lokacin da aka soma wannan rikici a 2020, yankin ya zama saniyar-ware daga sauran yankunan duniya sakamakon rashin wuta da kuma sadarwa.

Haka kuma babu hanyoyin intanet da na banki.

Ana zargin gwamnatin Habasha da saka takunkumi kan yankin wanda lamarin ya yi tasiri ga kai kayayyaki masu muhimmanci - lamarin da Habashar ta ɗora laifi kan yaƙin da ake yi.

Akwai dubban fararen hula da suka rasu, miliyoyi kuma suke cikin tsananin buƙatar abinci.

Shirin samar da abinci na Majalisar Ɗinkin Duniya ya ce kusan rabin mutum miliyan 5.5 da ke yankin Tigray na tsananin buƙatar abinci.

An koma da yaƙi a makon nan bayan an shafe watanni ana zaman lafiya sakamakon yarjejeniyar zaman lafiyar da aka cimmawa a watan Maris tsakanin gwamnatin Habasha da yankin Tigray domin bayar da dama a shigar da kayan agaji.

Ba wannan ne karo na farko ba da Mista Tedros wanda tsohon ministan lafiya ne a Habasha ke magana a kan wannan yaƙi ba.

Ko a ranar Laraba sai da ya ce yanayin yaƙin na Habasha ya fi na Ukraine ƙazanta inda ya ce wariyar launin fata ce ta sa ake nuna bambanci kan yadda duniya ke ɗaukar lamarin.

A 2020, Mista Tedros ɗin ya musanta zargin da ake masa na taimaka wa yan tawayen Tigray sayen makamai.

Akwai wasu ƴan yankin Tigray ɗin da suna shan wahala wurin neman ƴan uwansu kamar yadda Mista Tedros ke sha.

Wani mai bincike kuma masanin tattalin arziki wanda yake zama a wata ƙasa, Kibrom Abay ya bayyana cewa tura kuɗi zuwa Tigray abu ne mai matuƙar wahala da tsada sakamakon dakatar da ɓangarorin hada-hadar kuɗi a yankin.

"Ganin cewa ba zan iya taimaka wa iyayena waɗanda suka dogara a kaina ba abu ne mai ciwo," in ji shi.

Wani da ke zaune a Addis Ababa, babban birnin Habasha ya shaida wa BBC cewa sun samu wani wanda zai iya kai musu kuɗi Tigray idan an ba shi kamasho na kashi 20 cikin dari.

"An tsara abin ne ta yadda kuɗin za su isa cikin mako guda. An shafe sama da mako guda kuma iyalaina ba su samu kuɗin ba. Ban san halin da suke ciki ba a yanzu,'' in ji shi.