Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Da alama Lewandowsk zai iya zama warakar Barcelona
Bayan wani garari da dimauta da Barcelona ta shiga a kakar da ta gabata, sakamakon fitar wasu daga cikin manyan 'yan wasanta, za a iya cewa yanzu Barcelona ta samo bakin matsalarta.
Fitar babban dan wasanta Lionel Messi ya jefa kungiyar cikin laluben wanda zai maye wagegen gibin da ya bari.
Ko da yake a watan Fabirairu da ya gabata ta sayo dan wasan gaban Gabon Pierre-Emerick Aubameyang wanda kuma ya taka rawar ganinsa wajen ganin ya ceto kungiyar daga halin da ya sameta.
Da taimakon dan wasan kungiyar tikiti na halartar gasar Champions League.
Ta kuma kara sayen 'yan wasa da dama ciki har da Robert Lewandowski wanda ta dauka daga Beyern Munich, wanda ake gani zai iya zama waraka ga kungiyar.
Ko a ranar Laraba da kungiyar ta buga wasanta na farko da Viktoria Plzen sai da dan wasan ya ci kwallo uku karon farko tun dawowarsa kungiyar.
Dan wasan mai shekara 34 dan kasar Poland ya nuna kimar da yake da ita a kungiyar inda ya ci kwallo takwas cikin wasa biyar da ya buga bayan barinsa Bayern a watan Yuli.
Lewandowski, wanda ya taimaka wa Bayern ta lashe gasar 2019-20, ya fara buga wasansa na farko a Barcelona a gasar zakarun nahiyar Turai da kafar dama.
Da wadannan kwallaye magoya bayan Barcelona sun fara jin cewa dan wasan zai iya zama warakar matsalar da suka fada tun bayan rabuwa da Messi.
Sai dai wasu na ganin shekaru za su iya zama koma baya ga dan wasan a wannan lokaci.