Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Zaben Osun: 'Mu kuri'armu ta kudi ce'
Wasu masu kada kuri’a a zaben gwamnan Jihar Osun da ke kudu maso yammacin Najeriya sun bayyana cewa kuri’un nasu na sayarwa ne.
A yau Asabar ne ake gudanar da zaben wanda masu sharhi ke cewa zai yi zafi musamman tsakanin jam’iyyar APC mai mulki da PDP mai hamayya.
Wasu mutane da BBC ta tattauna da su, sun bayyana cewa duk da cewa suna da katin zabe, ba lallai ba ne su kada kuri’unsu idan "ba a ba mu kudi ba."
Mustapha Akibu, wani mazaunin Osogbo baban birnin jihar ta Osun, ya shaida wa BBC cewa, “A gaskiya ba a ba ni ko sisi ba, don haka ba zan ce komai ba, saboda ana ta raba kudi amma mu ba a ba mu ko sisi ba.”
Ya ce: “Zaben namu na yanzu a Najeriya ya riga ya canza, domin ko da ka yi saboda Allah, shirme ake dauka, don haka gara a ba ni kudi sai na je na kada kuri’ata tun da ana raba kudin.”
Matashin ya ce a halin da ake ciki zai iya sayar da kuri’arsa.
Ita ma wata mata da ba a bayyana sunanta ba, ta shaida wa BBC cewa, a gaya wa shugabanninsu cewa su yi aikin da aka ba su, kudin da aka ba su kuma, to su raba wa mutane.
Ta ce “Abin da zai hana mu yi zabe shi ne kudi, idan mun samu kudi sai mu je mu yi zabe.”
Sai dai kuma yayin da wasu ke cewa sai an ba su kudi za su yi zabe a jihar ta Osun, wasu kuwa sun ce ba sa bukatar a ba su ko sisi.
Wani matashi da BBC ta zanta da shi ya ce shi kuri’arsa ba ta sayarwa ba ce.
Ya ce shi wanda yake so zai zaba, don haka shi ba zai sayar da kuri’arsa saboda kudi ba.
Matashin ya ce, “Nawa za a ba ni da zan sayar da kuri’ata, kwata-kwata bai fi a ba ni naira dubu daya ba, don haka ni ba zan sayar da kuri’ata saboda kudi ba.”
Da dama dai masu sharhi kan harkokin siyasa a Najeriya na ganin tun a wurin zaben fitar da gwani a kasar 'yan takara ke fitowa da maitarsu a fili na ganin lallai sun ci zabe, hakan kan sa su fitowa da kudi domin rabawa masu kada kuri’a don su zabe su.
Akasari mata ne suka fi fitowa a lokutan zabe, kuma ana zargin 'yan siyasa na ba su sabulu da atamfofi ko kudi don su zabe su wanda haka na da illa sosai ga makomar matan a siyasance.
Sayar da kuri'a dai tamkar sayar da 'yancin dan kasa ne na tsawon shekaru hudu, kuma tsalle daya ake a fada rijiya, amma sai a yi dubu ba a fito ba.
Sannan bisa la'akari da halin da ake ciki a Najeriya, ya ishi 'yan kasar su yi karatun ta natsu tare da sauya tunani a kan yadda suke mika wuya ga 'yan siyasar da ke sayen kuri'a a lokutun zabe domin gudun fada wa hannun gurbatattun shugabanni.