Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Majalisar Dattijai ta fara tantance ministoci a Najeriya
Majalisar Dattijan Najeriya ta fara tantance mutanen da Shugaba Bola Tinubu ya aika mata don neman amincewarta kafin ya naɗa su ministoci.
Na farko a cikin mutanen da aka tura sunayensu su 28, shi ne Abubakar Momoh daga jihar Edo.
A matsayinsa na tsohon ɗan majalisar wakilai, Abubakar Momoh bai fuskanci tsauraran tambayoyi kafin Shugaban Majalisar Ɗattijai Godswill Akpabio ya buƙaci ya risina wa majalisa, ya wuce.
Mutum na biyu da ya bayyana a zauren majalisar, shi ne Nyesom Wike, tsohon gwamnan jihar Ribas.
Majalisar dai na sa ran tantance mutum 16 a ranar farko ta zaman da suke yi.
Haka kuma, ana sa ran Shugaba Tinubu zai aika da ƙarin sunaye, kamar yadda tsarin mulkin ƙasar ya yi tanadi kowace jiha daga cikin 36 na kasar za ta samu akalla minista daya.
Daga sunayen da Shugaban kasar ya mika wasu jihohin suna da mutum biyu yayin da wasu ba su da ko daya.
Bisa al'ada dai majalisar kan amince da wasu mutanen salun alun, da gaisuwa kawai yayin da wasu kuma kan sha tambaya.
Sanata Mohammed Ali Ndume, babban mai tsawatarwa na majalisar dattawan ya shaida wa BBC Hausa cewa Majaisar za ta yi taza da tsifa don tabbatar da ta sauke nauyin da ke kanta yadda ya kamata.
Sai dai ya ce kamar yadda aka saba bisa al'ada, wannan karon ma ba za a bata lokaci wajen tantance duk wanda ya taba zama Sanata a cikin sunayen da aka aika musu ba, domin idan har ka taba zama Sanata, to kuwa ka cika duk wani sharadi na zama minista ma.
Ya ce kafin a kawo sunayen ma dama jami'an tsaro na gudanar da bincike a kansu, domin tabbatar da cewa babu wata matsala
Ya kara da cewa ''Ni a ganina, wannan ce za ta kasance tantancewa mafi sauki, domin shi ma shugaban kasa tsohon Sanata ne, wanda ya aiko mana sunayen tsohon kakakin Majalisar wakilai ne, dukkansu sun san me ya kamata, don haka babu wata matsala da za a samu''.
''Al'adar mu ce wannan, idan kai sanata ne a da, idan ka zo za mu gaisa ne kawai ka tafi, ban san wanene ya ce za a samu wani banbanci ba yanzu'' a cewarsa.
Ya ci gaba da cewa 'So so ne, amma ai son kai ya fi, yanzu a ce ko ni gobe idan na zo gaban 'yan uwana sanatoci su tantance ni a kan wani mukami su tozarta ni ?, ai hakan ba dai-dai bane'' inji shi.
Mutanen da za a tantance ranar Litinin
1. Sen.Abubakar S.Kyari - Borno
2. Abubakar Eshiokpekha Momoh - Edo
3. Nyesom Ezenwo Wike - Rivers
4, Engr. Prof. Joseph Terlumun Utsev - Benue
5. Sen. John Owan Enoh - Cross River
6. Hon. Bello Muhammad - Sokoto
7. Mohammed Badaru Abubakar - Jigawa
8. Amb.Yusuf Maitama Tuggar - Bauchi
9. Sen. Abubakar Sani Danladi - Taraba
10. Barr. Uju-Ken Ohaneye - Anambra
11, Hon. (Dr). Olubunmi Tunji-Ojo - Ondo
12. Dr. Betta C.Edu Cross River
13. Imaan Sulaiman Ibrahim - Nasarawa
14. Arch. Ahmed Musa Dangiwa - Katsina
15. Chief Uche Geoffrey Nnaji - Enugu
16. Stella Erhuvwuoghene Okotete - Delta