Andreas Pereira zai koma Fulham daga Man United
Sabuwar kungiyar da za ta buga Premier League a bana, Fulham ta amince za ta dauki dan wasan tawagar Brazil, Andreas Pereira daga Manchester United kan fam miliyan 10 .
Pereira, mai shekara 26, ya buga wasannin aro a Flamengo a kakar da aka kammala, yana daf da saka hannu kan kwantiragin kaka uku a Cottagers.
Ya koma United a 2012, sai dai ya kasa samun gurbin buga wasanni sosai, inda aka bayar da shi aro ga Granada da Valencia da kuma Lazio.
Pereira ya yi wsa 74 a kungiyar Manchester United da cin kwallo hudu.
Pereira zai zama na biyu da Fulham ta dauka a bana, bayan Joao Palhinha daga Sporting Lisborn da aka saya kan fam miliyan 17.
Fulham za ta buga Premier League a bana, bayan da ta fafata a Champions League a kakar da ta wuce.

Asalin hoton, Getty Images







