Zanga-zanga na neman mamaye titunan ƙasar Peru

Asalin hoton, Reuters
Fusatattun magoya bayan shugaban Peru da aka tsige mai sassaucin ra'ayi Pedro Castiyo sun yi arangama da jami'an tsaro a daidai lokacin da zanga-zanga ta kacame a faɗin ƙasar.
Aƙalla mutum mutum biyu suka rasu a lardin Apurimac da ke kudancin ƙasar, haka kuma jama'a da dama sun raunata sakamakon tarzomar da ta kunno kai. A ranar Laraba ne Majalisar Dokokin ƙasar ta tsige Mista Castiyo bayan shafe watanni 16 kacal kan mulki.
A halin yanzu Mista Castiyo wanda ake zargi da cin hanci da kuma ƙoƙarin rushe majalisar dokokin ƙasar na garƙame a hannun ƴan sandan na Peru.
Magoya bayansa sun ce zarge-zargen da ake yi masa, masu ƙarfin faɗa a-ji a ƙasar ne kawai suka ƙiƙire su saboda irin rawar jikin da suke yi ta karɓar mulki.
Haka kuma an ci gaba da irin wannan zanga-zanga a babban birnin ƙasar wato Lima.
Ƴan sanda sun harba hayaƙi mai sa hawaye a ranar Lahadi domin tarwatsa masu zanga-zanga a birnin.
Haka kuma masu zanga-zangar sun yi wa 'yan sanda hamsin da wasu ma'aikatan gwamnati kawanya a filin jirgin saman Andahuaylas.
Hotunan da ake yadawa a shafukan sada zumunta na nuna hayaki na tashi a filin jirgin saman, wanda ke kudancin kasar.
Hukumar da ke kula da sufurin jirgin sama ta kasar CORPAC ta ce an lalata wasu bangarori - kuma an cinna wa gine-gine wuta a filin jirgin saman - a sanadiyyar barkewar mummunar zanga-zangar.











