...Daga Bakin Mai Ita tare da Wilson Onaze na Daɗin Kowa

...Daga Bakin Mai Ita tare da Wilson Onaze na Daɗin Kowa
An wallafa

A filin namu na ..Daga Bakin Mai Ita na wannan mako za mu kawo muku tattaunawa da Wilson Onaze na wasan Daɗin Kowa.

An dai haifi Wilson a birnin Kano kuma a nan ya yi makarantar firamare da sakandire har zuwa jami'a.

Ya fara harkar fina-finai a 2001 saboda "abin da nake so sosai ne" in ji Wilson.

Wilson ya ce scene ɗin da ya fi so a wasan Daɗin Kowa shi ne wanda "na fito daga gidan Madam Gloria aka ƙwace min waya."