Man City ta doke Man United ta lashe Community Shield

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 2

Manchester City ta lashe Community Shield na bana, bayan doke Manchester United a bugun fenariti 7-6 ranar Asabar a Wembley.

Ƙungiyoyin na birnin Manchester sun tashi 1-1 a minti 90 da suka kece raini a wasan na buɗe labulen kakar 2024/25.

United ce ta fara cin ƙwallo ta hannun Alejandro Garnacho saura minti takwas a tashi daga karawar daga baya City ta farke a minti bakwai tsakani ta hannun Bernado Silva.

Ana buga Community Shield tsakanin wadda ta ɗauki Premier League a bara da wadda ta lashe FA Cup.

City ce ke rike da Premier League, wadda ta ɗauka a kakar da ta wuce kuma na huɗu a jere.

United ce ke rike da FA Cup, bayan da ta doke City 2-1 a cikin watan Mayu a Wembley, wadda ta samu gurbin shiga Europa League da za a kara a bana.

Za a fara buga Premier League kakar 2024/25 ranar Asabar 16 ga watan Agusta, inda makon farko za a fara da karawa 10.

Wannan shi ne karo na bakwai da City ta lashe Community Shield, bayan 1937, 1968, 1972, 2012, 2018 da kuma 2019.

Tun daga lokacin da Pep Guradiola ya karɓi aikin horar da City a 2016/17, ya lashe kofi 18, ciki har da Premier League shida da FA Cup biyu da League Cup huɗu.

Sauran sun haɗa da Champions League da Uefa Super Cup da Fifa Club World Cup, yanzu ya ɗauki Community Shields na uku.

Wasannin makon farko a Premier League

Juma'a 16 ga watan Agusta 2024

  • Man Utd da Fulham a Old Trafford

Asabar 17 ga watan Agusta 2024

  • Ipswich da Liverpool a Portman Road, Ipswich
  • Arsenal da Wolves a Emirates Stadium, London
  • Everton da Brighton a Goodison Park
  • Newcastle da Southampton a St. James' Park
  • Nott'm Forest da Bournemouth a The City Ground
  • West Ham da Aston Villa a London Stadium

Lahadi18 ga watan Agusta 2024

  • Brentford da Crystal Palace a Gtech Community Stadium
  • Chelseada Man City a Stamford Bridge

Litinin 19 ga watan Agusta 2024

  • Leicester da Tottenham a King Power