Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Ƴan wasa bakwai sun mutu a hatsarin mota a zambia
Hukumar ƙwallon ƙafa ta Zambia (Faz) tana zaman makoki bayan da wasu ƴan wasa bakwai na ƙungiyar Chavuma Town Council FC suka mutu a wani hatsarin mota.
A wata sanarwa da ta fitar hukumar ta bayyana matukar kaɗuwarta kan hatsarin, wanda ya afku a ƙarshen makon da ya gabata, a lokacin da ƴan wasan ke tafiya gasar ƙwallon ƙafa a arewa maso yammacin ƙasar.
Shugaban Faz Andrew Kamanga ya ce "Muna tuntubar hukumomin kwallon kafa, farar hula da jami'an tsaro a lardin don ba mu cikakkun bayanai."
Wasu mutane 12 sun jikkata a hatsarin, kuma an kwashe biyar daga cikin su zuwa Lusaka babban birnin ƙasar domin yi musu magani.
Kawo yanzu dai ba a bayyana sunayen waɗanda hatsarin ya shafa ba.
Shugaban hukumar ƙwallon ƙafa ta Afirka (Caf) Patrice Motsepe ya bayyana alhini kan lamarin inda ya ce yana fatan wadanda suka jikkata za su murmure nan ba da jimawa ba.