Betis ta samu maki uku kan Real a La Liga karon farko bayan 2020

Asalin hoton, Getty Images
Real Betis ta doke Real Madrid 2-1 a wasan mako na 26 a La Liga ranar Asabar a Benito Villamarin.
Real ce ta fara cin ƙwallo minti 10 da fara tamaula ta hannun Brahim Diaz, haka suka je hutu ana cin Betis 1-0.
Bayan da suka yi hutu suka koma zagaye na biyu ne Betis ta farke ta hannun Johnny Cardoso daga baya Isko ya kara na biyu a bugun fenariti.
Wannan shi ne karon farko da Betis ta haɗa maki uku a kan Real tun bayan nasara 2-1 a gida ranar Lahadi 8 ga watan Maris 2020.
Real Madrid ta doke Real Betis 2-0 a wasan farko a Bernabeu ranar 1 ga watan Satumba, Kylian Mbappe ne ya ci ƙwallayen ta biyu a bugun fenariti.
Ɗan wasan Betis, Antony mai buga wasannin aro daga Manchester United ya buga fafatawar, bayan da aka soke jan katin da aka yi masa.
Tun farko an kori ɗan kasar Brazil a wasan da Betis ta doke Getafe, daga baya ƙungiyar ta ɗaukaka kara aka soke hukuncin.
Sai dai Real ta buga karawar ba tare da Jude Bellingham ba, wanda karo na biyu ke hukuncin dakatarwa, bayan jan katin da aka yi masa a 1-1 da Osasuna a Fabrairu.
Alkalin wasa, Jose Munuera Montero ne ya rubuta a rahotonsa bayan tashi daga karawar cewar ɗan wasan tawagar Ingila ya faɗa masa kalaman da ba su dace ba.
Real Madrid tana mataki na biyu a teburin La Liga da maki 54, sai dai Atletico za ta iya zama ta ɗaya da zarar ta yi nasara a kan Athletic Club ranar Asabar.
Ranar Lahadi Barcelona za ta karɓi bakuncin Real Sociedad a wasan na mako na 26.
Wasan da ke gaban Real na gaba shi ne Champions League da za ta fafata da Atletico ranar Talata 4 ga watan Maris a Bernabeu.
Ƴan wasan Real Madrid:
Masu tsare raga: Courtois, Lunin da kuma Fran González.
Masu tsare baya: Alaba, Lucas V., Fran García, Rüdiger, Mendy da kuma Asencio.
Masu buga tsakiya: Camavinga, Modrić, Tchouameni, Arda Güler da kuma Chema.
Masu cin ƙwallaye: Vini Jr., Mbappé, Rodrygo, Endrick da kuma Brahim.









