PSG da Real na zawarcin Alexander-Arnold, Liverpool na neman Amar Dedic

Asalin hoton, Getty Images
Paris St-Germain (PSG) da Real Madrid na fafatawar neman ɗaukar ɗan wasan bayan Liverpool mai shekara 26, Trent Alexander-Arnold. (Fichajes - in Spanish)
Liverpool ta tuntuɓi RB Salzburg game da ɗan wasan bayan ta ɗan ƙasar Bosnia/Herzegovina mai shekara 22, Amar Dedic, wanda ake sa ran zai maye gurbin Alexander-Arnold. (Caught Offside)
Wolves na shirin ɗaukar ɗan wasan tsakiyar Watford da Georgia, Giorgi Chakvetadze, mai shekara 25 a watan Janairu. (Sun)
Shugaban Real Madrid na tsara yadda zai maye gurbin kocin ƙungiyar, Carlo Ancelotti da kocin Bayer Leverkusen, Xabi Alonso. (Sport - in Spanish)
Tsohon ɗan wasan gaban Italiya, Mario Balotelli, mai shekara 34, zai yi gwajin lafiya a ƙungiyar gasar Seria A, Genoa a ranar Litinin, kuma ana sa ran zai ƙulla yarjejeniya da ƙungiyar bayan ya yi gwajin. (Fabrizio Romano)
West Ham na sha'awar ɗan wasan gaban Atalanta da Nigeria, Ademola Lookman, mai shekara 27, a wani mataki da kocin ƙungiyar, Julen Lopetegui ya ɗauka domin ƙarfafa tawagarsa a watan Janairu. (GiveMeSport)
Manchester City ta shirya tsawaita kwangilar ta da ɗan wasan bayan Croatia, Josko Gvardiol, mai shekara 22, wadda za ta kai ta kuɗi £150,000 a kowanne mako, kuma za ta ba shi damar ci gaba da taka leda a ƙungiyar har zuwa 2030. (Star)
Ɗan wasan tsakiyar Ingila da Chelsea mai shekara 22, Cole Palmer, zai ci gaba da taka leda a Chelsea, duk da jita-jitar da ke alaƙanta shi da komawa wata ƙungiyar. (Football Insider)
AC Milan na neman mayar da ɗan wasan gefen Liverpool da Italiya, mai shekara 27, Federico Chiesa zuwa gasar Seria A (Caught Offside)
Watakil tsohon ɗan wasan Jamus, Mats Hummels, mai shekara 35, zai bar Roma a watan Janairu duk da cewa bai daɗe da komawa ƙungiyar ta gasar Seria A ba. (Nicolo Schira)











