Real Madrid na son Fernandez daga Chelsea, Ƙungiyoyin Firimiya na rububin Gibbs-White

Asalin hoton, Getty Images
Real Madrid na farautar ɗan wasan Chelsea mai shekara 24 daga Argentina da ke buga tsakiya, Enzo Fernandez a sabuwar kaka. (Teamtalk)
Chelsea na iya amincewa Fernandez ya koma Madrid a wani bangare na musayarsa da ɗan wasan Faransa mai shekara 25, Aurelien Tchouameni. (Four Four Two), external
Real Madrid na kuma zawarcin ɗan wasan Bournemouth, mai shekara 19 Dean Huijsen, wanda ke bugawa ajin yara matasa a Netherlands kafin ya koma wakilta Safiniya rukunnin 'yan kasa da shekara 21. (AS - in Spanish)
Liverpool da Arsenal da kuma Manchester United na cikin ƙungiyoyin da ke farautar ɗan wasan tsakiya a Nottingham Forest da Ingila, Morgan Gibbs-White, mai shekara 25. (Caughtoffside)
William Saliba ba shi da niyyar barin Arsenal duk da cewa Real Madrid ta shirya biyan makudai kan ɗan wasan na Faransa mai shekara 23. (Fabrizio Romano)
Arsenal na bibbiyar yarjejeniyar saye ɗan wasan Newcastle mai shekara 27 daga Brazil, Bruno Guimaraes a wannan kaka. (Sun)
Coventry City ta shiga rububin saye ɗan wasan Netherlands, Tyrese Asante mai shekara 22, daga Maccabi Tel-Aviv. (Sky Sports)
Crystal Palace tayi nisa a tattauna sabon yarjejeniya da ɗan wasan Ingila mai shekara 29, Will Hughes, da kwantiraginsa ke karewa lokacin bazara. (Football Insider)
Ɗan wasan gaba na Palace a Faransa, Jean-Philippe Mateta mai shekara 27, na cikin 'yan wasa hudu da Manchester United ta kwallafa rai a kansu a lokacin bazara. (TeamTalk, external)
Liverpool ta bi sahun Arsenal a farautar ɗan wasan Faransa mai shekara 17, Ayyoub Bouaddi bayan bajinta da ya nuna a Lille a wannan kaka. (TBR Football)
Ɗan wasan Roma da Ingila, Tammy Abraham mai shekara 27, wanda ke zaman aro a AC Milan, ya fadawa abokansa cewa burinsa ya koma Aston Villa a wannan kaka. (Football Insider)
Liverpool na ta binciken wanda za ta dauko domin maye gurbin ɗan wasanta na baya mai shekara 31, Scot Andy Robertson inda kuma mai tsaron baya a Bournemouth Milos Kerkez, mai shekara 21 ya shiga jerin wadanda take hari. (Mail - subscription required)











