Isra'ila ta amince ta tsagaita wuta saboda riga-kafin polio a Gaza

    • Marubuci, Tom Bennett
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News
    • Aiko rahoto daga, London
  • An wallafa
  • Lokacin karatu: Minti 3

Hukumar Lafiya ta Duniya, WHO, ta ce Isra'ila ta amince ta tsagaita wuta a Gaza domin ta bayar da dama a yi wa yaran Zirin allurar riga-kafin polio.

Ana sa ran za a yi wa yara kusan 640,000 allurar, wadda za a fara gabatarwa ranar Lahadi, kamar yadda wani jami'in WHO, Rik Peeperkorn ya bayyana.

Za a gudanar da shirin allurar ne a zagaye uku, a yankin tsakiyar Zirin Gaza da kudanci da kuma arewacin yankin.

A duk matakin allurar, za a daina yaƙi a yankin na kwana uku tsakanin ƙarfe 06:00 zuwa 15:00 na agogon yankin.

An cimma yarjejeniyar ce bayan Majalisar Dinkin Duniya ta ce wani yaro mai kimanin wata 10, ya kamu da shanyewar ɓarin jiki bayan kamuwa da cutar polio na farko a Gaza bayan shekara 25.

Tuni alluran riga-kafin miliyan 1.2 na nOPV2 suka isa Gaza, sannan ana sa ran ƙarin 400,000 nan da wani ɗan lokaci.

Jami'an Majalisar Dinkin Duniya da wasu ma'aikatan kiwon lafiya na Zirin ne za su yi aikin allurar.

Tuni aka horar da ma'aikatan lafiya sama da 2,000 domin gudanar da aikin.

Kakakin Majalisar Dinkin Duniya a Gaza, Louise Wateridge ta ce akwai buƙatar a tsagaita wuta a yankin domin a samu damar yin allurar lami lafiya.

"Ba zai yi wu mu yi wa yara allura ba ana jefa bama-bamai. Ba za mu iya yi musu allurar ba alhalin suna guje-gujen tsira daga hare-hare domin tsira da rayukansu," kamar yadda ta bayyana wa Radio 4's a ranar Juma'a.

"Matuƙar za a kawo hare-hare a lokacin da muke gudanar da aikin allurar, dole zai shafi aikinmu," inji ta.

Ms Wateridge ta ce za a yi wa yaran allura biyu cikin mako guda, sannan za su buƙaci a yi musu wata allurar nan da mako huɗu.

Hukumar Lafiya ta Duniya ta ƙuduri aniyar cimma kashi 90 na allurar riga-kafi a Zirin Gaza, wanda ake matuƙar buƙata domin hana yaɗuwar cutar a yankin.

Cutar polio na da saurin yaɗuwa, kuma ta fi yaɗuwa ta ruwan kwatami da gurɓataccen ruwa.

Cutar kan janyo shanyewar ɓangaren jiki, sannan tana iya kisa. Ta fi shafar ƙananan yara ƴan ƙasa da shekara biyar.

WHO ta ce kafin fara yaƙin, an samu nasarar riga-kafi a Gaza da Gaɓar Yamma da Kogin Jordan.

An ƙiyasta cewa an cimma kashi 99 na allurar riga-kafin a yankin a 2022, duk da cewa ya koma kashi 89 a bara, kamar sabuwar ƙididdiga ta nuna.

Ita ma Isra'ila ta faɗa a watan Yuli cewa ta fara yi wa sojojinta riga-kafin cutar.

Wani jami'in Hamas, Basem Naim ya shaida wa Reuters cewa, "a shirye muke mu haɗa gwiwa da ƙungiyoyin duniya domin samun nasarar wannan shiri na riga-kafin domin kare rayuwar sama da yara 650,000 a zirin Gaza."

Sai da Firaiministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu ya ce ajiye kari da za su yi na wata uku, "ba tsagaita wuta" ba ne.

James Kariuki, mataimakin wakilin MDD na dindindin na Birtaniya a MDD ya ce, "ya ji daɗin shirin allurar da za a fara."

"Ya kamata a ce tsagaita wutar ta wuce haka domin a samu nasarar cimma kashi 90 na allurar. Idan aka fara shirin, dole a kare yaran da za su wajen allurar," inji shi.

Farfesa Hagai Levine, wanda shi ne kakakin ƙungiyar ƴan uwan waɗanda ake tsare da su wato Hostages Families Forum - wadda take fafutikar ganin an sako mutanen Isra'ila waɗanda Hamas ke tsare da su- ya ce akwai buƙatar masu aikin allurar su haɗa da waɗanda ake tsare da su a yankin.

Idan ba a manta ba, Isra'ila ta ƙaddamar da yaƙi a Gaza ne tun bayan harin Hamas a Kudancin Isra'ila a 7 ga Oktoba, inda ake kashe mata mutum 1,2000, sannan aka kama tare da tsare mata mutun 251.

An kashe sama da mutum 40,530 a Gaza tun bayan fara yaƙin, kamar yadda Ma'aikatar Lafiyar yankin da ke ƙarkashin Hamas ta bayyana.