Mece ce cutar polio kuma yaya take yaɗuwa?

Mece ce cutar polio kuma yaya take yaɗuwa?
An wallafa

Ku latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon:

A baya-bayan nan an gano ƙwayar cutar polio a kwatami a wasu manyan biranen duniya.

Cutar, wacce ba a faye samunta ba, wata ƙwayar cuta ce ke samar da ita, kuma a yanzu an kusa kawar da ita a duniya.

Cutar na yaduwa ne idan mai ɗauke da ita ya taɓa marar ita - ko kuma ta hanyar gurɓataccen ruwa ko abinci - ko kuma ta hanyar atishawa da tari.

Wannan bidiyon an yi shi ne albarkacin ranar yaki da cutar polio ta duniya da ke faɗowa duk ranar 24 ga watan Oktoban 2022.