Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Falasɗinawa nawa aka kashe tun bayan fara yaƙi a Gaza?
Ma’aikatar lafiyar Hamas da ke Gaza ta ce fiye da Falasɗinawa 40,000 aka kashe sakamakon hare-haren sojojin Isra’ila a Gaza tun bayan harin 7 ga watan Oktoban bara da Hamas ta kai.
Adadin - wanda ya kai 40,005 ya zuwa ranar Alhamis – ya kai kusan kashi 1.7 na mutum miliyan 2.3 da ke zaune a Gaza – wani adadi da ke nuna irin ararar rai da da yaƙi ya janyo.
Baya ga asarar rayukan, hotunan tauraron ɗan’adam sun nuna yadda kusan kashi 60 na gine-ginen Gaza suka ruguje ko lalace tun bayan fara yaƙin.
A watannin baya-bayan nan birnin rafah da ke kudanci ƙasar, ya fuskanci mafi yawan ruguje-rugujen, kamar yadda hotuna suka nuna.
Alƙaluman da ma’aikatar lafiyar Hamas ɗin ta fitar, bai bambance takanin fararen hula da mayaa ba.
To sai dai bayanan da aka gan sun nuna cewa ma fi yawan waɗanda suka mutum mata ne da ƙananan yara da kuma tsofaffi.
A wannan wata, rundunar sojin Isra’ila ta shaida wa BBC cewa fiye da ƴanta’adda 15,000 aka kashe a lokaci yaƙin.
Isra’ila ta hana ƴanjaridar duniya ciki har da na BBC shiga cikin Gaza bisa raɗin kansu, don haka ba za a iya tantance alƙaluman duka ɓangarorin ba.
A lokutan yaƙe-yaƙen baya, Majalisar Ɗinkin Duniya da sauran gukumomin duniya na ɗaukar alƙaluman da ma’aikatar lafiyar Hamas ke fitarwa a matsayin hujja abin dogaro.
Takan ƙirga mutanen da asibitoci suka tabbatar da mutuwarsu kaɗai, bayan sanya sunayensu da na lambobinsu da sauran bayanansu cikin rajistar mutanen da suka mutun.
To amma a ƙarshen shekarar da ta gabata, ma’aikatar ta kasa yin aikinta yadda ya kamata, bayan cikar ɗakunan adana gawarwakin asibitocin yankin, da kuma yai da kusa da asibitocin da rashin kyawun intanet da na waya.
Ofishin yaɗa labaran Hamas a Gaza ya fara wallafa adadin mutanen da suka mutu, ciki har da amfani da rahotonnin da ‘’yardaddun kafofin’’ yaɗa labarai suka fitar.
Hukumomin Majalisar Dinki Duniya sun fara sanya waɗannan bayanai cikin alƙaluman da suke tattarawa tare da na ma’aikatar lafiyar a duk lokacin da ta sabunta su.
A baya-bayan nan ma’aikatar lafiyar Hamas ta fara ƙirga mutanen da ‘yan uwansu suka bayar da rahoton kashe su a shafukan intanet.
Haka kuma suna ƙirga gawarwakin mutanen da ba za a iya gano su ba cikin adadin mutannen da aka kashe.
A yanzu Majalisar Dinkin Duniya ta ambata waɗannan alƙaluma, inda jami’ai ke danganta su, sannan su ake jaddada cewa abokan aikinsu da ke Gaza ba za su iya tabbatar da adadin ba, saboda yanayin da ake ciki a yankin da kuma yawan kashe-kashen da ake yi a yankin.
Isra’ila tana yawan sukar ingancin bayanan. A watan Mayun da ya gabata ne, ministan harkokin wajen ƙasar Israel Katz ya bayana alƙaluma da “bayanan ƙarya daga kungiyar ta’addanci”.
To amam masana da dama na cewa haƙiƙanin adadin mutanen da aka kashe a yaƙin ka iya zarta wannan adadi da yawa gaske, yayin da jami’an yankin ke ƙiyasta cewa akwai kusan gawarwaki 10,000 da gine-gine suka danne sakamakonhare-haren Isra’ila.
Kuma duk da ba a iya dakatar da yaƙin ba, masu bincike sun ce baya ga adadin mutanen da suka muta sakamkon yain kai-tsaye, akwai kuma wasu da dama da za su iya mutuwa sakamokon illar da yaƙin ya haifar musu, kamar yunwa ko cutuka.
Daga ƙarshe idan aka kammala yaƙin, ƙoƙarin nemo gawarwaki da mutanen da sua ɓace zai bayar da damar samun cikakun alƙaluman waɗnda aka kashe, ciki har da adadin mayaƙan.
Ana sa ran Majalisar Dinkin Duniya da ƙwararru da kuma sojojin Isra’ila kowannensu zai gudanar da bincike na ƙashin kai game da batun.
Hotunan tauraron ɗan’adam sun nuna cewa kusan kashi 59.3 na gine-ginen Gaza sun lalace ko sun ruguje tun bayan fara yaƙin.
Sharhin ɓarnar gine-ginen yankin da Corey Scher na jami’ar City da ke birnin New York da Jamon Van Den Hoek na jami’ar jihar Oregon, sun yi ƙoƙarin kwatanta hotunan domin nuna irin canjin da aka samu kan tsayi ko tsarin gine-ginen.
Binciken masanan ya nuna cewa birnin Rafah da ke kudancin ƙasar ya fi kowane yanki fuskantar ɓarnar in cikin watan Maris.
Mafi yawan uguje-rugujen sun auku ne hare-haren da Isra’ila ta ƙaddmar kan birnin ranar 6 ga watan Mayu. Sojojin Isra’ila sun ce ƙwace iko da yankin da kuma kakkaɓe sauran rundunonin Hamas na daga cikin muhimman manufofin yaƙin nata.
Hotuna tauraron ɗa’adam da sashen tantance bayanai na BBC ya yi nazarinsu, sun nuna yadda mafi yawan birnin ya ruguje, musamman kusa da kan iyakar Masar da sauran wuraren da ke arewaci da kudanci.
Hotuna da bidiyoyin da sojojin Isra’ila suka wallafa a shafukan sada zumunta da BBC ta tantance sun nuna yadda aka lalata ko aka ruguza wasu wurare a kusa da ta hanyar jefa boma-boma da jirage marasa matuƙa da kuma rushewar gine-ginen da sojojin Isra’ila suka yi ta ƙasa a yankin.
Wannan hoton da ke ƙasa na nuna wani ɓangare na gine-ginen da aka ruguje a kusa da kan iyakar.
Hotunan tauraron ɗan’adam sun nuna yadda aka share fili a yankin da ake kira ‘Philadelphi corridor’, wani wuri mai tsayin kilomita 14 a kan iayakar Masar.
Sharhin hotunan sashen tantance labarai na BBC sun nuna motocin sojojin Isra’ila a wurare da dama a yankin, inda aka share gine-gine a kusa da kan iyakar. Wanna ya haɗa da ƙananan garuruwan da kan iyakar.
A ƙasa kuma wani bidiyo da wani sojan Isra’ila ya ɗauak ya nuna yadda daga baya aka gina wata hasumiyar sojoji a yankin.
Hare-haren sun kuma lalata wasu muhimman wurare a Rafah, ciki har da mashigar Rafah da wasu masallatai masu yawa da kuma babbar kasuwar garin.
A ranar 7 ga watan Mayu, wani bidiyo da BBC ta tantance ya nuna wasu tankunan yaƙin Isra’ila ɗauke da rubutun ‘’Barka da zuwa Gaza’’ a kan iyakar Rafah.
Wani bidiyon da aka wallafa a wannan ranar ya nuna yadda lalata masallacin Abrar. Hotunnan tauraron ɗan’adam da aka ɗauka bayan hakan sun nuna yadda aka lalata gine-gine.
Hakama wani bidiyo da aka wallafa a shafukan sada zumunta ranar 27 ga watan Yuni ya nuna yadda wani titi da kuma kwalliyar da aka yi wa fitaccen shataletalen Al-Najma da ke Rafah suka ruguje, inda gine-ginen da ke kusa da wurin suka lalace.
A dai fara yaƙin ne lokacin da dubban mayaƙan Hamas suka kai samame kudancin Isra’ila ranar 7 ga watan Oktoba, suka kashe mutum 1,200 tare da yin garkuwa da wasu 251, kamar yadda Isra’ilar ta bayyana.