Tottenham ta amince za ta ɗauki Tel daga Bayern Munich

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Tottenham ta ƙulla yarjejeniyar ɗaukar matashin tawagar Faransa ta ƴan kasa da shekara 21, Mathys Tel daga Bayern Munich.

Har yanzu ba a fayyace ba ko za ta ɗauki aron ɗan wasan ne ko kuma sayen shi za ta yi.

Mai shekara 19, bai amince ya koma Tottenham ba, wadda tun baya ta yi zawarcinsa, amma yanzu ya yadda zai koma buga Premier League.

Mai kula da harkokin tamaularsa, Gadari Camara ya saka hoto a kafar sada zumunta da shi da Tel a cikin jirgin sama na alfarma.

Ranar Lahadi Tottenham ta je ta doke Brentford 2-0 a wasan hamayya a Premier League, wasa na takwas da ta ci daga karawa 24 kenan a bana.

Ƙungiyar da Ange Postecoglou ke jan ragama tana ta 14 a kasan teburin babbar gasar tamaula ta Ingila ta bana, ta kai zagaye na biyu a Europa League kai tsaye.

Ranar Alhamis Tottenham za ta buga wasa na biyu a Carabao Cup da Liverpool a Anfield, Tottenham ce ta ci 1-0 a wasan farko ranar 8 ga watan Janairu.

Idan har Tottenham ta kammala batun Tel zai zama na biyu da ta ɗauka a kwana biyu bayan Kevin Danso daga Lens.

Tun can baya an ta alakanta Tel da zai koma taka leda a Manchester United.