Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Ku San Malamanku tare da Farfesa Yahuza Abdullahi Muhammad
A wannan makon za mu kawo muku Sheikh Farfesa Yahuza Abdullahi Muhammad a filinmu na Ku San Malamanku wanda malami ne a birnin Maiduguri.
Farfesa Yahuza ya halarci makarantar harshen larabci da addinin Musulunci unguwar Agege da ke jihar Legas.
Malamin ya samu gurbin ƙaro karatu a ƙasar Syria inda daga baya ya koma ƙasar Libya domin samun shaidar karatun digiri.
Ya koyar a sashen koyar da Larabci a jami'ar da ke Maiduguri a jihar Borno inda kuma har yanzu a can yake koyarwa.
Shehun malamin ya yi karatu zaure da na zamani inda ya samu ilimi a wurin malamai da dama.
Farfesa ya ƙware a fannin harshen Larabci da fassara da kuma ilimin rabon gado.