Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Champions League: Inter za ta kara da Barca a daf da karshe
Inter Milan ta kai daf da karshe a Champions League, duk da tashi 2-2 da Bayern Munich a San Siro ranar Talata.
Tun farko ƙungiyar Italiya ce ta je ta ci Bayern 2-1 a makon jiya a wasan farko zagayen kwata fainal a gasar ta zakarun Turai.
Sun tashi ba ci a zagayen farko ranar Talata a Italiya, sai da suka sha ruwa suka koma zagaye na biyu ne aka ci dukkan ƙwallayen.
Harry Kane ya fara cin ƙwallo daga baya Inter ta farke ta hannun Lautaro Martinez da Pavard, sai kuma Bayern ta farke ta hannun Dier.
Da wannan sakamakon Inter za ta kara gida da waje da Barcelona a daf da karshe a Champions League.
Barcelona ta fitar da Borussia Dortmund ta kawo zagayen daf da karshe a gasar zakarun Turai, karon farko tun bayan 2019.
Barcelona ta doke Dortmund 4-0 a Sifaniya a makon jiya, sannan ta yi rashin nasara 3-1 a Jamus ranar Talata.
Daya wasan daf da karshe za a yi ne tsakanin Arsenal da Paris St Germain.
Arsenal ta kai zagayen gaba, sakamakon fitar da Real Madrid, kuma karon farko da Gunners za kai daf da karshe bayan 2009.
Ita kuwa Paris St Germain, wadda ke fatan lashe Champions League a karon farko a tarihi, ta fitar da Aston Villa ne.