Abubuwa biyar masu amfani da ake samarwa daga ƴaƴan kaɗanya

Ƴaƴan kaɗanya

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Ƴaƴan kaɗanya
An wallafa
Lokacin karatu: Minti 5

Najeriya ta sanar da haramta fitar da ɗanyen ƴaƴan kaɗanya daga ƙasar zuwa ƙasashen waje na tsawon watanni shida.

Gwamnatin ƙasar ta ce ta ɗauki matakin ne domin ƙara bunkasa kasuwancin sa ganin cewa ta na asarar dukiya mai ɗimbin yawa saboda ba ta sarrafa shi yadda ya kamata a cikin gida.

An yi ittifaƙin cewa Najeriya na samar da kashi 40 na ƴaƴan kaɗanyan da ake samarwa a duniya, sai dai kasa da kashi ɗaya na dala biliyan 6 da miliyan 500 da ake samu daga kasuwancinsa duk shekara a faɗin duniya Najeriyar ke samu.

Sai dai gwamnatin ƙasar ta ce ba za ta lamunci hakan ba.

Najeriya ce kuma ƙasar da ta fi kowace samar da ƴaƴan kaɗanya a yammacin Afirka, inda akwai ƙasashe kamar Ghana da Burkina Faso da Mali da kuma Togo, waɗanda tuni ma suka hana fitar da ƴaƴan kaɗanyar zuwa ƙasashen waje.

Ƴaƴan kaɗanya abu ne da har yanzu bincike ke ci gaba da gano ɗimbin alfanun sa wanda ke sa ƙasashen waje ƙara buƙatar sa.

A Najeriya, an fi samun su ne a jihohin Neja da Kwara da Oyo, kuma akasari mata ne ke samo shi da kuma sarrafa shi a gargajiyance.

BBC ta tuntuɓi farfesa Kpotun Mohammed Baba, shugaban riko na cibiyar bincike kan ƴaƴan kaɗanya da ke jami'ar fasaha ta tarayya da ke Minna jihar Neja domin jin amfanin ƴaƴan kaɗanya da kuma yadda ake sarrafa shi ya zama abubuwan amfani da dama.

Farfesa Kpotun ya ce ƴaƴan kaɗanya na da matuƙar amfani a ciki da wajen ɗan'adam, sai dai a shekarun baya amfanin gida kawai ake yi da shi kamar girki da shafawa a jiki.

''A wannan zamanin, amfanin ƴaƴan kaɗanya ya fi ƙarfin amfanin gida sakamakon binciken da ake ci gaba da yi'' in ji shi.

Ya kuma jero mana abubuwa biyar masu muhimmanci da ake yi da ƴaƴan na kaɗanya:

Magani

Man kaɗe a gefen ƴaƴan kaɗanya a kan koren ganye

Asalin hoton, Getty Images

Wani abu da binciken masana ya bankaɗo shi ne yadda za a yi amfani da ƴaƴan kaɗanya wajen haɗa magunguna na gargajiya da kuma na zamani.

''Kin san wasu sinadarai da ake haɗa magunguna da su ba sa iya daidaituwa da kansu, don haka idan aka yi amfani da wasu sinadaran ƴaƴan kaɗanya sai ya daidaita su,'' a cewar Farfesa Kpotun Mohammed .

Ya kuma ce ana daidaita sinadaran ne ta yadda ba za su cutar da ɗan'adam ba.

Haka nan sinadaran da ke cikinsa na maganin kumburi tare da taimakawa wajen warkewar gyambo, da kuma tallafa wa lafiyar zuciya.

Hakazalika a gargajiyance ma akan haɗa su da wasu magungunan domin yin amfani da su.

Man gashi da na wanke kai

Wasu mata uku su na sarrafa ƴaƴan kaɗanya.

Asalin hoton, Getty Images

Wani abu kuma da ake yi da ƴaƴan kaɗanya shi ne haɗa mayukan wanke gashi da kuma na shafawa a gashin.

Mai bincike kan ƴaƴan kaɗanya, farfesa Kpotun ya shaida wa BBC cewa yin amfani da shi a gashi na taimakawa wajen gyara gashi da hana shi karyewa da kuma sa shi ya yi laushi saboda yana ƙunshe da sinadarai kamar Vitamin A.

''Musamman ma mata, su suka fi amfani da shi kuma ya na taimaka musu sosai,'' in ji shi."

Haka nan man kaɗe na hana gashi bushewa ko kuma maido wa gashi danshinsa bayan bushewa.

Yana kuma hana ɗagawar fatar da ke a ƙasan gashi da kare faruwar 'dandruf, sannan kuma yana sanya gashi tsawo.

Abinci

Yadda ake sarrafa ƴaƴan kaɗanya a gargajiyance a Najeriya

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Yadda ake sarrafa ƴaƴan kaɗanya a gargajiyance a Najeriya

Tun bayan lokacin da aka gano ƴaƴan kaɗanya, girki na daga cikin abubuwan da aka fara yi da man da ake samu daga cikin su.

Farfesa Kpotun ya ce ƴaƴan kaɗanyan na tattare da wasu sinadarai kamar 'fatty acids', da 'Vitamins' da wasu da ke taimakawa wajen sanya kuzari a jikin ɗan'adam, da ba shi kariya daga cutuka, da gina jiki da kuma ƙara lafiyar jiki baki ɗaya.

"Su na da sinadaran 'Stearin' da 'Olein' da ke da amfani a jiki,'' kamar yadda ya yi wa BBC bayani.

Man shafawa don hana tsufa da gyaran jiki

Man kaɗe, mai ne sananne da akan shafa a jiki ga manya har ma da ƙananan yara.

Akan shafa shi shi kaɗai ko a haɗa shi cikin wasu mayukan domin amfanin yau da kullum.

A cewar Farfesa Kpotun Muhammad, man kaɗe na ƙunshe da sinadaran 'vitamins A da E da kuma F' wadanda ke taimakawa wajen inganta tafiyar jini a jikin ɗan'adam da kuma tsirar fata mai lafiya.

Man kade na samar da sanadaran da ke hana tsufa da taimakawa wajen gyara fata, da kuma ba ta launi mai kyau da santsi.

Haka nan yana da sinadaran da ke kashe ƙuraje tare da kuma bayar da kariya.

Sinadarin Steric acid da ke ƙunshe a cikin man kaɗe yana taimakawa wajen kaurara mayukan shafawa.

Kayan kwaliyya

Ƙwararriyar mai sana'ar kwalliya Zainab Hassan

Asalin hoton, Zainab Hassan

Bayanan hoto, Ƙwararriyar mai sana'ar kwalliya Zainab Hassan

Ƙasashen kamar Jamus da Netherlands da Japan da Birtaniya da ma Amurka suna amfani da ƴaƴan kaɗanya wajen yin kayan kwaliyya.

Kayan kwalliyar da ake haɗawa da man kadanya sun haɗa da man shafawa a leɓe da sabulun wanka da man da ake sahafawa a fuska.

Yin cakuleti

Cakuleti

Asalin hoton, Getty Images

Ƙasashen Turai sun bayar da damar amfani da ƴaƴan kaɗanya a madadin ƴaƴan koko da kusan kashi 5 wajen haɗa chakulet, wanda a cewar Farfesa Kpotu, hakan ne ya ƙara buƙatar sa da ake da shi a ƙasashen waje.

'' Sun yi hakan ne saboda ya fi koko arha, kuma ya na ƙara mishi daɗi da sinadaren gina jiki'' in ji masanin.