Ko United za ta iya lashe gasar Europa?

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Bayan nasarar da ƙungiyar Manchester United ta samu a kan ƙungiyar Lyon ta Faransa, inda ta samu tsallakawa matakin wasan gab da na ƙarshe a gasar Europa, yanzu tambayar da ake yi ita ce shin za ta iya lashe gasar?

Abin da masu sharhi kan wasanni na kafar TNT suka tattauna ke nan bayan wasan da aka fafata a filin wasan, wanda aka fafata a Old Trafford.

A nasa jawabin, Darren Fletcher ya ce, "dole mutum ya fara tunanin ko an rubuta sunan ƙungiyar a kofin na Europa (lashe kofin) bayan nasarar da ta samu a kan Lyon."

A nasa ɓangaren, tsohon kyaftin ɗin ƙungiyar, Rio Ferdinand ya ce ƙoƙarin da ƴanwasan ƙungiyar suka yi a wasan na jiya ne ya sa ya fara canja tunani.

"Bayan yau (Alhamis) zai yi wahala mutum ya yi tababar cewa Manchester United za ta iya lashe gasar."

Manchester United ta kai zagayen kusa da ƙarshe ne bayan doke Olympic Lyon ta Faransa da 5-4, bayan an yi canjaras da 2-2 a wasan farko da aka buga a Faransa. Ke United ta yi nasara da 7-6 jimilla.

Yanzu United za ta fafata wasan gab da na ƙarshe ne da ƙungiyar Athletic Bilbao a ranar 21 ga watan Mayu.

Ƙungiyar ta Bilbao ta kai wasan ƙarshe a gasar Europa sau biyu, na ƙarshen a shekarar 2012, lokacin da Atletico Madrid ta doke ta da ci uku da nema a Bucharest.

Shekara 13 ke nan rabon United ta haɗu da Athletic Bilbao, inda ƙungiyar ta Spain ta doke United da 2-1 a gasar ta Europa a shekarar 2012.

Ita kuma United wannan ne karo na biyu da za ta buga wasan gab da na ƙarshe a gasar Europa a shekara huɗu.

A wancan karon, Manchester United ta doke Roma da ci 8:5 jimilla.

Sai dai ƙungiyar Villareal ta doke ta a wasan ƙarshe a bugun fanareti bayan an tashi wasan kunnen-doki.