Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Ƙalubale biyar da ke gaban Tinubu
- Marubuci, Buhari Muhammad Fagge
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Multimedia Journalist
- Aiko rahoto daga, Abuja
- An wallafa
Ko wanne matakin rayuwa dai na zuwa ne da ƙalubale kamar yadda masana ke faɗa, nasara ko akasinta.
Haka lamarin yake ga nasarar da sabon shugaban Najeriya mai jiran gado Bola Ahmed Tinubu ya samu, kuma zai fuskanta.
Da yawa na yi wa nasararsa kallon mai tattare da ƙalubale waɗanda ba za su ƙirgu ba, waɗanda ya gada tun daga lokacin da aka dawo tsarin dimokraɗiyya a jamhuriya ta huɗu a Najeriya a 1999.
Ga wasu ƙalubale biyar da ake ganin su ne waɗanda zaɓaɓɓen shugaban zai fuskanta, kuma suke buƙatar a mayar da hankali kansu cikin gaggawa:
Sauya fasalin naira
Sabon zaɓaɓɓen shugaban Najeriyan zai zo ya tarar da matsalar rashin kuɗi da ‘yan ƙasar suke fama da ita, saboda ƙarancin sababbin takardun naira da gwamnatin shugaba Buhari mai bankwana ta ɓullo da shi.
Wannan dai wani mataki ne da ake ganin ya shafi kowa a ƙasar, ta fuskar ‘yan kasuwa ya janyo tsayawar lamuran kasuwanci a birane da ƙauyuka saboda rashin tsabar kuɗi a hannu.
Ta fuskar ‘yan siyasa, ana ganin ya hana su rawar gaban hantsi, saboda abin da ake zargin ƴan siyasa da shi na amfani da kuɗaɗe lokacin zaɓe domin sayen ƙuri’a ko kuma sallamar ma’aikatan jam’iyya da suke aiki a lokutan zaɓe.
CBN da ya ɓullo da wannan tsari ne a rubu’in ƙarshen shekarar bara, ya bayar da gajeren wa’adi domin daina amfani da tsofaffin takardun naira tare da musanya su da sababbi.
Hakan dai ya janyo ce-ce-ku-ce daga kusan dukkan ɓangarorin al’umma, tare da kukan cewa akwai abubuwan da suka kamata a yi gabanin ɗaukar matakin.
CBN ya ce kimanin kashi 80 cikin ɗari na kudin da aka buga domin a riƙa mu’amala da su a ƙasar suna hannun mutane, kusan kashi 20 ne ke hannun bankunan kasuwanci da shi CBN.
Hakan na cikin dalilin da ya sa CBN ke son rage yawan kuɗin da ke yawo a tsakanin mutane, wanda ya ce hakan zai iya rge matsalar hauhawar farashin kayayyaki.
Wannan dai ya tayar da hankalin gwamnoni da dama na ƙasar abin da ya sanya wasunsu suka kai gwamnatin tarayya ƙara.
Gwamnan jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufa’i cikin wata tattaunawa da ya yi da BBC ya ce, CBN ya karɓi kimanin naira tirliyan 2.23 daga hannun al’umma, kuma ya buga naira biliyan 300 ne kawai, wanda wannan ba zai ishi ‘yan Najeriya su gudanar da harkokinsu ba.
Idanu na kan Tinuubu domin ganin mai zai yi kan wannan matsala da zai gada daga gwamnati mai ci.
Janye tallafin mai
Wani babban lamari da Najeriya ta shiga shekarar 2022 da shi kan shanin man fetur da cire tallafinsa shi ne wannan "Kamfanin mai na NNPC na buƙatar naira tiriliyan uku a 2022".
Daga lokacin hawa mulkin shugaban Najeriya na yanzu Muhammadu Buhari zuwa yau, an yi ta samun kwangaba-kwanbaya kan lamarin man fetur.
Kuma har zuwa yanzu babu sahihiyar magana kan cire tallafin.
Rashin tabbas kan sha'anin man dai ya haifar da dogayen layuka a gidajen sayar da mai, waɗanda a tarihi ba a samu lokacin da aka daɗe ana wuyar man fetur ba kamar wannan,
Kungiyoyin masu dakon mai da masu safararsa sun rika shan zargi kan cewa su ne ke haifar da matsalar man a faɗin Najeriya.
A baya sai da kungiyar IPMAN ta ce an musu ƙarin farashin man a hukumance, ƙasa da kwana 10 NNPCL ya musanta hakan.
A bara Kamfanin mai na Najeriya, NNPCL, ya ce ya nemi naira tiriliyan uku domin biyan kuɗin tallafin man fetur a shekarar 2022 bayan gwamnatin ƙasar ta fasa janye tallafin kamar yadda ta tsara a watan Yuni.
Ministar Kuɗi da Tsare-Tsare, Zainab Ahmed Shamsuna ce ta bayyana hakan, ta kuma ce gwamnatin tarayya na kashe kusan naira biliyan 270 a kowane wata wajen biyan tallafin man fetur, wanda hakan abu ne da ba zai dore ba.
A ƙarshen 2022 gwamnatin ta ce tabbas za ta cire tallafin, Amma za ta soma cire tallafin man fetur ɗin ne daga Afrilun 2023, wato watanni uku kafin ainahin lokacin da aka yi niyyar cire tallafin a baya.
"Abin da ya fi shi ne wannan gwamnatin watakila ta soma cire tallafi a farkon zango na biyu na wannan shekara saboda zai fi nagarta idan aka cire a hankali a maimakon a jira a cire shi baki ɗaya," in ji ministar.
Sai dai tun lokacin da yake yaƙin neman zaɓensa, zaɓaɓɓen shugaban ƙasar Bola Ahmed Tinubu ya sha alwashin janye tallafin man fetur da zarar ya zama shugaban kasar.
"Dokar man fetur tana nan kuma za mu duba ta a karo na biyu domin sauke nauyin da ke kanmu kuma duk zanga-zangar da za a yi, za mu cire tallafin man fetur," in ji Tinubu.
Ya kara da cewa: "Za mu dauki matakai masu tsauri, wannan shi ne batun gaskiya. Don haka wajibi ne mu cire tallafin man fetur."
Tinubu ya bayyana matsayarsa a wannan fanni, sai dai a jira a ga yadda zai aiwatar da kalaman nasa.
Rashin tsayayyen farashin dala a Najeriya
Wani wuri da aka gaza samun daidaito a cikinsa shi ne harkar musayar kuɗaɗen ƙetare, musamman tsakanin dala da naira.
Ko da yake za a iya cewa gwamnati ba ta da ruwa a cikin harkokin canji kai tsaye tun bayan da ta dakatar da bai wa masu kamfanonin kasuwancin kuɗaɗen ƙetare dalar da take ba su daga CBN.
Amma gabanin dakatar da ba su dalar, farashinta ya tsaya ne a naira 459.94 a matsayin na hukuma, yayin da a yanzu farashinta a kasuwa yakai 760.
Wannan rashin daidaito na haifar da tashin farashin kayayyaki da kuma rashin tsayayyen farashi.
Ƙananan abubuwan da za ka iya saye a baya yanzu sun yi tsadar da ba za su sayu ba, saboda tashin farashin.
Da dama da ke kasuwancin ƙasa da ƙasa yanzu ba su iya safara saboda babu dalar, balle a iya saya, in kuma aka samu, farashinta zai haura yadda mutum in ya sayo kayanshi ba zai iya cin riba ba.
Talauci
Wani rahoton da bankin duniya ya fitar a watan Disambar 2022, ya ce kimanin mutum miliyan 95 na rayuwa cikin talauci a Najeriya.
Rahoton da aka yi wa suna "Fashin baƙi kan makomar tattalin arzikin Afirka," ya mayar da hankali ne kan bayanan da hukumomin cikin gida ke fitarwa lokaci zuwa lokaci kan abin da ya shafi taluci.
A rayuwar da mutane ke ciki yanzu a Najeriya da dama na shan wuya wajen gudanar da rayuwarsu ta yau da gobe, abubuwa da dama ba su samuwa saboda ƙarfin talauci.
Duk da cewa gwamnatin Shugaba Buhari ta ɓullo da shirye-shiryen rage talauci a ƙasar, amma har yanzu ana fama da shi.
Sai dai da yawa na ganin matsalar annobar korona ta ƙara ta'azzara wannan matsalar.
Amma za a jira a ga mene ne sabon shugaban zai yi domin rage talauci da yawan matalauta a ƙasar.
Rabuwar kai
Zaɓen shugagan ƙasar da aka gudanar a Najeriya ranar 25 ga watan Fabirairu ya haifar da koma baya ga Najeriya, idan aka yi la’akari da doguwar tafiya da ta yi a baya, wadda ta fara kakkaɓe siyasar ɓangaranci da addini da ƙabilanci.
Zaɓen ya haifar da rabuwar kawuna tsakanin masu zaɓe da shugabanni da kuma su kansu jam’iyyun siyasar.
Malaman manyan addinan ƙasar na Kirista da na Musulunci sun shiga siyasar kai tsaye tare da bayyana ɗan takarar da suke so mabiyansu su zaɓa.
Ta ɓangaren masu zaɓen kuwa sun riƙa bayyana cewa mutumin da ya fito daga yankinsu ko kuma ɗan ƙabilarsu ko wanda suke addini ɗaya ne kawai za su zaɓa, in ba haka ba sai dai su bar zaɓen.
An riƙa samun sa-in-sa tsakanin ‘yan ɓangaren kudancin ƙasar da arewaci a kafafen sada zumunta musamman bayan zaɓen.
An riƙa ɗauko kalaman da wasu magoya bayan Peter Obi suke yi gabanin zaɓe ana zolayarsu da su, su kuma suna mayar da maganganu marasa daɗi a matsayin ramuwa ga ‘yan yankin arewaci.
Wannan dai ya fito da matsalar rabuwar kai da ake da ita ƙarara a ƙasar, wadda kuma take buƙatar a dauki matakin gaggawa a kanta.
Koda yake sabon shugaban ƙasar a lokacin jawabinsa na murnar lashe zaɓe, ya yi alƙawarin aiki tare da duka ‘jam’iyyun adawa da waɗanda suka fafata tare da shi a yayin neman zaɓen, ba tare da nuna banbanci ba.