Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Abin da ya sa APC ta dakatar da kaddamar da yakin neman zaben shugaban kasa
Jam`iyyar APC mai mulkin Najeriya ta yi karin haske a kan dalilin da ya sa ta dakatar da shirinta na kaddamar da yakin neman zaben shugaban kasa da `yan majalisun dokoki.
Jam`iyyar ta ce tana so ne ta fadada gangamin yakin neman zaben ta yadda kowane dan jam`iyyar zai ji cewa ana damawa da shi.
Tun da farko APC ta tsara za ta fara yakin neman zaben ne ranar Laraba. Wasu rahotanni dai sun ce akwai wasu jiga-jigan jam`iyyar, ciki har da gwamnoni, wadanda ba su ji dadin gangamin da aka hada tun da farko ba.
Yadda jam`iyyar APC ta yi shelar kaddamar da yakin neman zaben da kuma yadda ta sake sanar da dage ranar duka a cikin kwana guda ya sa wasu sun fara zargin cewa da walakin, goro a miya musamman ma yadda jam`iyyar ta dage ranar karo daya ana washegari za a fara yakin neman zaben, wanda ta tsara a gobe Laraba za a yi wana zama na adu`o`i da tattaki a cikin birnin tarayya.
Amma jam`iyyar ta ce ba matsala ba ce ta sa aka fasa, illa tana so ne ta kara kyautata shirin da take yi, kamar yadda Honorabul Dattuwa Alin Kumo, dan kwamitin gudanarwar jam`iyyar APC, ya shaida wa BBC.
"Ba janyewa aka yi ba; ka san siyasa abu ne na yawun jama'a da ake bukatar kowa da kowa. Zabe ake so a shiga na shugaban kasa kuma ba shi kadai muke so mu ci ba. Muna so mu ci zaben gwamnoninmu da sanatocinmu da 'yan majalisar dokoki, don haka ba ma so mu bar baya da kura," in ji Honorabul Alin Kumo.
Ya kara da cewa babban abin da ya sa suka sauya ranar kaddamar da yakin neman zaben shi ne a tabbatar an tuntubi kowanne mai ruwa da tsaki a jam'iyyar ta yadda zai sanya hannu a kamfe din zaben.
Tun lokacin da dan takarar shugaban kasa na jam`iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu, ya fitar da jerin sunayen mutanen da ke cikin gangamin yakin neman zaben aka yi ta samun bayanai da ke nuna cewa akwai wasu jiga-jigan jam`iyyar da aka mai da su saniyar-ware.
Kazalika wasu rawar da aka nemi su taka ba ta wuce ta rufe-baki ba ko irin na tashi-ka-faye-nacin nan, ciki har da wasu gwamnonin jihohi. Bayanai sun nuna cewa hakan ya fusata su.
Irin wannan zargi ya yi karfi lokacin da aka fahinci cewa har da sunan mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo da Sakataren gwamnatin tarayya a cikin wadanda aka yi kashi aka manta da su.
Kodayake wasu mukarraban Shugaba Buhari sun ce shugaban kasar ne ya bukaci a yi hakan.
Da dama dai ana tsammanin cewa jam`iyyar APC ta dakatar da kaddamar da gangamin ne domin ta sake sabon zubi.
Amma Honorabul Dattuwa Alin Kumo ya ce suna da fahinta a tafiyar tasu. "Wannan duk ba shi ba ne. Dan adam zai iya yi kuskure ya kuma gyara balle a siyasa," a cewarsa.