Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Taƙaddama ta ɓarke a APC bayan fitar da ƴan kwamitin yaƙin zaɓen 2023
Jam’iyyar APC mai mulki a Najeriya ta yi ƙarin haske game da cece-ku-cen da ake yi musamman a shafukan sada zumunta na internet kan jerin sunayen tawagar yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa da ta fitar.
Ƙananan maganganu sun fara ɓulla ne bayan da aka ga babu sunayen wasu jiga-jigan jam'iyyar a cikin jerin sunayen, ciki kuwa har da mataimakin shugaban ƙasa Yemi Osinbajo - wani abu da masana ke ganin zai iya barin baya da ƙura.
Jaridar Premium Times ta ruwaito cewa wasu gwamnoni na jam’iyyar APC sun yi barazanar yin zagon kasa ga yaƙin neman zaɓen ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar, Bola Tinubu, a jihohinsu.
Gwamnonin sun zargi Mista Tinubu da ƙin karɓar mutanensu a kwamitin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasar.
Sakataren kwamitin yaƙin neman zaɓen James Faleke, ya ce kafin a saki jerin sunayen tawagar kamfe din, sai da shugabannin kwamitin suka tuntubi gwamnonin don su zaɓi mutanen da za a saka a tawagar daga jihohinsu, inda aka buƙaci su bayar da sunan mutane biyar.
Sai dai jaridar ta ce gwamnonin sun sha matuƙar mamaki da ganin yadda Tinubu ya sauya mutanensu da wasu a jihohin nasu ba tare da tuntuɓarsu ba.
Bala Ibrahim shi ne Daraktan yaɗa Labaran Jam'iyyar kuma ya shaida wa BBC cewa ba lalle ba ne a ga sunan kowa da kowa a cikin jerin sunayen mambobin kwamitin saboda "an kafa kwamiti ne domin taimakawa, kuma ba wai ana nufin mutum ɗaya shi zai iya komai ba, inda ka ji an ce mataimaki, akwai wani sama da shi,"
"A wannan kwamiti an duba an ga babu sunan shugaban ƙasa?, idan akwai shugaban ƙasa, maganar mataimaki ya shigo ba ta taso ba," a cewar Bala Ibrahim.
Ya bayyana cewa tun bayan fitar da jerin sunayen, jam'iyyar ba ta yi wata ganawa a kan lamarin ba.
A cewarsa, an kafa kwamitin domin tsara dabarun neman ƙuri'ar ƴan Najeriya saboda akwai buƙatar waɗanda sunayensu ba sa cikin kwamitin su karkatar da kansu ga ayyuka masu muhimmanci.
Ya ce akwai yiwuwar a samu sauye-sauye a Jam'iyyar - "bayan wannan kwamitin, akwai wasu ƙananan kwamatoci da za a kafa na shiyya-shiyya, akwai wasu waɗanda ba lalle ba ne a ga sunansu ɓaro-ɓaro cikin kwamiti.
"Amma rawar da suke takawa tana da yawa, wataƙila sune fitilar da ke haska wa wannan kwamiti hanya ya ga inda zai bi."
Hangen masana kan turka-turkar
Tuni masana suka fara tsokaci game da wannan mataki da ya janyo turka-turka. Dr Abubakar Kari na Jami'ar Abuja a Najeriya ya ce ƙaramar magana za ta iya zama babba idan gaggan Jam'iyyar ba su yi da gaske ba.
"Jam'iyyar ba ta da zaɓi sai ta fito da dabaru da hanyoyin magance wannan abu, idan ba haka ba, zai yi mata illa a zaɓukan da suke ƙaratowa, a takaice irin illar da za a masa shi ne za a kakkaɓe masa magoya baya.
"Za a yi amfani da batutuwa na addini a yi masa zagon ƙasa a sa mutane su ƙyamace shi suƙi zaɓensa." in ji masanin.