Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
An tabbatar da mutuwar zaratan sojojin Rasha dubu 50
- Marubuci, Olga Ivshina
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Russian Service
- An wallafa
Adadin sojojin Rasha da suka mutu a UKraine ya ƙaru zuwa 50,000 - kamar yadda BBC ta tabbatar.
A cikin watanni 12 na shekara ta biyu da fara wannan rikici - yayin da Moscow ke cewa tana ƙara kutsa kai cikin ƙasar- an samu ƙaruwar mace-mace da kashi 25 sama da wanda aka samu a shekarar farko.
Sashen Rasha na BBC da wata kafar yaɗa labarai mai zaman kanta da ake kira Mediazona da wasu 'yan sa kai sun riƙa ƙirga mutanen da suka mutu tun watan Fabirairun 2022.
Sabbin kabura a maƙabartu sun taimaka wajen samar da sunayen wasu sojojin.
Tawagarmu ta tattaro bayanai daga wurare daban-daban daga rahotannin hukumomi da jaridu da kafafen sada zumunta.
Sama da sojojin Rasha 27,300 ne suka mutu a shekara ta biyu ta fara yaƙin - a binciken da muka yi - an gano yadda yunkurin kama iyaka ya janyo asarar rayukan al'umma.
Rasha dai ta yi watsi da wannan iƙirari.
Rasha na amfani da wani salo na nika abokan gaba wanda take aikewa da sojojinta filin yaƙi domin gano inda dakarun Ukraine suke a fada wa masu amfani da makaman atilari.
Duka mutuwar ta haura 50,000 - wanda ya ninka adadin da mahukunta suka amince suka shaida wa mutane a Moscow a watan Satumbar 2022.
Da yiwuwar adadin sojin Rasha da suka mutu su zarce haka yawa.
Masu fashin baƙinmu ba su sanya mutuwar mayakan da suke Donetsk da Luhansk da Rasha ta mamaye - A gabashin Ukraine. Kaga idan da ƙari adadin wadanda aka kashewa Rasha babu shakka ya zarce haka.
Da wuya Ukraine ta faɗi adadi mutanen da aka kashe mata. A watan Fabrairu, Shugaba Zelensky ya ce an kashe sojojin Ukraine 31,000 - amma a hasashen da hukumar leken asirin Amurka adadin ya wuce haka.
Ƙirga kabura
Ma'aikatan da suke aikin sa kai tare da BBC da kuma Mediazona sun riƙa ƙirga sabbin kabura a maƙabartu 70 a faɗin Rasha tun bayan fara rikicin.
An riƙa fadada maƙabartu cikin gaggawa kamar yadda ake iya gani a hotunan tauraron ɗan adam.
Hotuna da bidiyon da aka ɗauka sun nuna mafi yawan sabbin kaburan na sojojin da jami'ai ne da aka kashe a Ukraine.
BBC ta yi kiyasin cewa biyu cikin mayaƙan Rasha biyar da ake kashewa ba su da wata alaƙa da sojojin ƙasar gabanin su fara mamaya a Ukraine.
A farkon mamayar da aka yi a 2022, Rasha ya yi amfani da kwararrun sojojinta wajen kai hare-hare masu rikitarwa - kamar yadda Samuel Cranny-Evans na Cibiyar Rusi ya yi bayani.
Yanzu mafi yawan waɗannan kwararrun sojojin ko dai sun mutu ko kuma an musu munanan raunuka, kamar yadda mai sharhi kan tsaron ya bayyana, an kuma maye gurbinsu da mutanen da masu kai su kwarewa ba da kuma ƙarancin samun horo - kamar mayakan sa kai, fararen hula da kuma fursunoni.
Wadan nan mutanen ba za su iya abin da kwararrun za su yi ba, in ji Cranny-Evans.
"Wannan na nufin duk abin da za su yi za su yi shi ne da karancin dabaru kamar kwararrun."
Wagner da ma'aikatar tsaro
Wadanda aka riƙa dauka daga gidan yari sun riƙa taimakawa wajen murƙushe 'yan hamayya - masu sharhinmu sun ce su ake yawan kashewa cikin gaggawa a fagen yaƙi.
Moscow ta bai wa Yevgeny Prigozhin damar ɗaukar mayaka daga gidan yari a watan Janairun 2022.
An mayar da fursunonin mayaƙa sannan suƙa riƙa yaƙi a matsayin mayaka masu zaman kansu da ke yaƙi a madadin gwamnatin Rasha.
Wagner sun riƙa ɗar-ɗar kan rashin imanin da sukai ƙaurin suna a kai ga zunzurutun ƙeta da suke nunawa wajen horo.
Kai tsaye ake kashe sojojin da suka yi gaban kansu ba tare da bin umarni ba.
Tawagar ta ci gaba da ɗaukar mayaƙan har zuwa Fabirairun 2023, yayin da alaƙarta da Moscow ta fara tsami.
Tun daga nan, Ministan tsaron Rasha ke aiwatar da manufa irin wannan.
Prigozhin ya jagoranci wani boren soji da aka daƙile a watan Yuni bara - kuma suna yi yunkurin kutsa kai Moscow gabanin a dakatar da su.
An kuma kashe shi wani haɗarin jirgin sama a watan Agusta.
Sharhinmu na baya-bayan nan ya mayar da hankali ne kan sunayen fursunonin Rasha 9,000 wadanda aka kashe a fagen daga.
Sama da su 1,000, mun tabbatar da lokacin da kwataraginsu ya ƙare da kuma lokacin da aka kashe su.
Mun samu wannan ne ta hannun Wagner, wadannan tsofaffin sun tsira ne na aƙalla watanni uku.
Akwai kuma wadanda ma'aikatar tsaro ta ɗauka da suka rayu na watanni biyu kacal.
Ma'aikatar ta ƙirƙiri wani sashe na gama-gari da ta kira tsawar dakaru, wanda kusan duka wadanda aka yankeewa hukunci ne cikinsa.
Kamar dai irin sashen da Wagner ta ƙirƙira ne, wannan wani sashe ne da aka ce an fadada daga dakarun da suke ya ki a fagen daga.
A baya-bayan nan, an yi amfani da mayaƙan a watannin da suka gabata wajen kama birnin Andiivka.
Birnin ya koma ƙarƙashin Rasha makonni takwas da suka gabata kuma wannan wata gagarumar nasara ce ga Putin tun bayan kama Bakhmut da ya yi a baya.
An riƙa aika fursunoni fagen daga kai tsaye
A ƙarƙashin Wagner, ana bai wa sabbin fursunoni horon makonni biyu gabanin a tura su fagen daga.
Idan aka kwatanta, mun gano wasu sabbin fursunoni da aka kashe a filin yaƙi a mako biyun farko na kwantaraginsu.
BBC ta tattauna da iyalan fursunonin da aka kashe - da kuma sojojin da suke a raye - wadanda suka shaida mana atisayen da aka bai wa fursunonin na makonni biyu ba ya isa.
Wata wadda mijinta ya mutu, ta shaida mana mijinta ya sanya hannu kan kwantaraginsa da ma'aikatar tsaron ranar 8 ga watan Afrilun bara - kuma yayi yaƙin kwana uku ne kawai kan a kashe shi.
Ta ce ta yi ta jiran ta ji kira daga gare shi, amma daga baya ta gano an kashe shi ranar 21 ga watan Afrilu.
'A shirya mutuwa '
Yayin aiki a ƙarƙashin Wagner, ana ɗaukar fursunonin ne aikin watanni shida.
Duk wanda ya samu nasarar tsira da ransa cikin watanni shida sai a ba shi 'yanci ya tafi ya ci gaba da rayuwa.
Amma tun daga watan Satumbar bara, duk fursinan da aka ɗauka zai yi ta yaƙi ne har sai ya mutu, ko kuma an kammala yakin - wanda dai ya fara zuwa a wurinsa.
Wani labari da BBC ta rika samu a baya-bayan nan shi ne, fursunonin sun riƙa kiran 'yan uwansu suna neman su saya musu cikakkun kayan soji da takalman yaƙi.
An riƙa samun labaran wasu fursunonin da ake kai wa yaƙi ba tare da ba su cikakkun kayan aiki ba, ko magunguna ko kuma bindigogi masu kyau.
"Da yawan sojojin na da bindigogin da ba za su ɗauki lokaci ana yaƙi da su ba," kamar yadda wani mai wallafa abubuwa a intanet mai goyon bayan Rasha ya wallafa a Telegram.
"Me soja zai yi a fagen daga bayan ba shi da kayan yaƙi da na magani, babu ramukan shiga a buya, sannan bindigogin ma duk sun karye, wannan wane irin tashin hankali ne!"
"Makaman da ake bai wa fursunonin da kuma kayan sojojin ba za su iya yiwa soja komai ba."
Wani tsohon fursuna ya bayyana irin wuyar da abokansu suka sha.
"Idan har ka sanya hannu yanzu, to ka shira mutuwa," in ji Sergei, ya wallafa a wani zauren intanet da mayaƙan suke musayar bayanai.
Ya yi ikirarin shi tsohon fursuna ne da yake yaƙi tun watan Oktoba.