Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Man City ta kai wasan karshe a FA Cup bayan cin Chelsea
Manchester City ta kai wasan karshe a FA Cup, bayan da ta ci Chelsea 1-0 ranar Asabar a Wembley.
City mai rike da FA Cup na bara ta kawo wannan matakin, bayan da ta fitar da Newcastle United, ita kuwa Chelsea ta yi waje da Leicester City ce.
Bernardo Silva ne ya ci kwallon bayan da Kevin de Bruyne ya buga masa tamaular, saura minti shida a tashi wasan.
Wannan nasarar ta faranta ran City, bayan da aka yi waje da ita a Champions League a hannun Real Madrid a bugun fenariti a Etihad ranar Laraba.
City mai rike da Champions League na bara ta yi ban kwana da gasar zakarun Turai a zagayen daf da na kusa da na karshe.
Chelsea za ta yi da na sanin karawa da City, bayan da ta kasa amfana da damar makin da ta samu musamman ta hannun Nicolas Jackson.
Karo na biyu da Chelsea ta rasa kofi a bana a Wembley, bayan da Liverpool ta doke ta a wasan karshe ta lashe Carabao Cup na kakar nan.
Haka kuma kungiyar Stamford Bridge ta yi korafin fenariti da cewar bugun tazara da Cole Palmer ya buga ta taba hannun Jack Grealish a cikin katanga.
Na'urar da take taimakawa alkalin wasa yanke hukunci wato VAR ce ta fayyace ba bugun daga kai sai mai tsaron raga bane.
City, wadda ta lashe kofi uku a bara na kan turbar daukar biyu a bana, wato FA Cup da Premier League.
Kungiyar Etihad za ta jira wasan karshe da duk wadda ta yi nasara tsakanin Coventry City da Manchester United da za su yi ranar Lahadi 21 ga watan Afirilu a Wembley.