Ko kun san makomar masu adawa da Putin?
Akwai makoma guda ɗaya ga wadanda suka ƙalubalanci Shugaba Vladimir Putin a Rasha.
Dukkan su sun yi mutuwar da take da alamar tambaya.
Alexei Navalny (1976 - 2024)
Alexei Navalny na ɗaya daga cikin masu ƙalubalantar Putin.Wanda miliyoyin mutane a intanet suka kalli bidiyan bincikien da yake yi- ya zama barazana.
Mutuwar bazata da ya yi a gidan yari a Siberian ya zama babban labari a fadin duniya.
Yevgeny Prigozhin (1961 - 2023)
Sannan ba da daɗewa ba Yevgeny Prigozhin, wanda a baya masoyi ne amma ya koma mai hamayya da gwamnatin Putin, a shekarar 2023.
Ya mutu a wani hatsarin jirgi a wani yanayi mai ban mamaki bayan watanni.
Boris Nemtsov (1959 - 2015)
Boris Nemtsov ɗan adawane na jam’iyyar hamayya.
An harbe shi sau huɗu a baya.
Anna Politkovskaya (1958 - 2006)
Yar jarida Anna Politkovskaya ta ƙalubalanci yan sandan kasar Russia.
An harbe ta a shekarar 2026.
Alexander Litvinenko (1962 - 2006)
Sannan tsohon dan leken asirin KGB Alexander Litvinenko wanda yake ƙalubalantar Putin.
Ya mutu a birnin Landan bayan ya sha kofin shayin da maaikatan Rasha suka sa wa guba.
Pavel Antov (1957 - 2022)
Dan kasuwa Pavel Antov wanda ya karyata cewa shi ne mafarin saƙon Whatsapp da ya janyo yakin Ukraine.
Amma lokaci kaɗan bayanan nan, ya mutu ta hanyar faɗowa daga taga a ɗakinsa na otel a Indiya.
Ravil Maganov (1954 - 2022)
Ravil Maganov, wanda yake ƙalubalantar yaƙi a Ukraine - ya faɗo daga taga amma wannan karon a birnin Mascow.
Amma fadar Kremlin ta musanta duk wani zargi da hannu a wadannan kasha-kashen.
Amma fadar Kremlin ta musanta duk wani zargi da hannu a wadannan kasha-kashen.



