Ku San Malamanku tare da Sheikh Abdulmumini Ibrahim

Ku San Malamanku tare da Sheikh Abdulmumini Ibrahim
An wallafa

Shirin Ku San Malamanku na wannan makon ya tattauna da Sheikh Abdulmumini Ibrahim wanda aka fi sani da Mallam Na'ibi Gombe.

An haife shi a garin Rano, cikin jihar Kano ranar 15 ga watan Yunin 1964.

Ya fara karatunsa na makarantar allo a hannun mahaifinsa, kamar yadda suka gada a gidansu na Sarkin Malaman Rano.

Sai da ya yi saukar karatun Alƙur'ani kafin a sanya shi a makarantar firamare da ke yammacin Je-Ka-Da-Fari.

Malaman da ya tasirantu da su akwai Sheikh Sa'idu Imma da Sheikh Halau Lau da Sheikh Yusuf da sauransu.