Matan da bala'in fari ya tilasta musu sayar da shanunsu

Bayanan bidiyo, Danna hoton da ke sama domin kallon bidiyon:
Matan da bala'in fari ya tilasta musu sayar da shanunsu
An wallafa

Mata 'yan kabilar Maasai a Kenya suna daukar hotunan yadda fari yake shafar rayuwarsu.

Wata kungiya mai zaman kanta ce ta ba su kyamarori domin daukar hotunan irin bali'in da sauyin yanayi ya haddasa a yankunansu.

Lamarin dai ya sa suna sayar da wasu shanunsu domin saya wa sauran abincin da za su ci saboda ciyawa ta yi karanci.