Celta Vigo ta kori koci Benitez bayan kusan wata tara kan aiki

An wallafa

Celta Vigo ta raba gari da koci, Rafael Benitez, bayan kusan wata tara yana kan aikin.

Benitez mai shekara 63, tsohon kociyan Liverpool da Chelsea da Real Madrid ya koma horar da kungiyar Sifaniya ranar 23 ga watan Yunin bara.

Ya kuma bar kungiyar bayan nasara biyar a fafatawa 26 a lik da ya ja ragamar Celta.

Hakan ya sa kungiyar tana ta 17 a teburin babbar gasar tamaula ta Sifaniya da tazarar maki biyu tsakaninta da 'yan ukun karshen teburi.

Karon farko da Benitez ya ja ragamar kungiyar tamaula tun bayan da Everton mai buga Premier League ta sallame shi a Janairun 2022.

A wasa 33 a dukkan karawa da ya ja ragamar Celta ta ci wasa tara, kuma uku daga ciki ya fuskanci kananan kungiyoyi uku a Copa del Rey.

Wasan karshe da ya ja ragama Celta shi ne 4-0 da Real Madrid ta yi nasara ranar Lahadi a Santiago Bernabeu.

Celta Vigo za ta buga wasan gaba a La Liga ranar Lahadi da za ta ziyarci Sevilla.

Benitez ya lashe Champions League a 2005 da FA Cup a 2006 da Liverpool da Europa League a 2013 lokacin da ya horar da Chelsea.

Ya kai Newcastle United gasar Premier League daga Championship a 2016/17, ya kuma horar da Valencia da Inter Milan da kuma Napoli.