Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Lionel Messi ya lashe kyautar Ballon d'Or karo na takwas jimilla
Lionel Messi ya lashe kyutar gwarzon dan kwallon kafa na duniya na 2023, wato Ballon d'Or karo na takwas jimilla.
Messi tsohon dan wasan Barcelona da Paris St Germain mai taka leda a Inter Miami a Amurka ya dauki kofin duniya a Qatar a 2022.
Shi ne ya ja ragamar Argentina ta lashe babban kofin duniya na farko a wajensa, sannan na uku a kasar jimilla.
Aitana Bonmati ce ta zama gwarzuwar kwallon kafa ta 2023, wato macen da ta lashe Ballon d'Or.
Bonmati, mai shekara 25, ta dauki Champions League da kofin Sifaniya a Barcelona a bara - da lashe kofin duniya a bana tare da tawagar Sifaniya.
Sam Kerr ta Chelsea da Australia ce ta biyu, sai 'yar kwallon Barcelona da tawagar Sifaniya, Salma Paralluelo ce ta uku.
Karo na takwas kenan da Messi ke lashe kyautar ta Ballon d'Or, bayan da ya dauka a 2009, 2010, 2011, 2012, 2015, 2019 da kuma 2021.
Sai dai ya lashe kyautar 2021 tare da Robert Lewandowski, ya kuma yi wa Cristiano Ronaldo tazara mai biyar da ya ci a 2008, 2013, 2014, 2016 da kuma 2017).
Masu uku-uku a tarihin karbar kyautar Ballon d''Or sun hada da Michel Platini da Marco van Basten da kuma Johan Cruyff.
Karim Benzema ne ya lashe kyautar bara lokacin yana taka leda a Real Madrid, a kakar da Messi bai kai bantensa ba cikin 'yan takara.
Wasu na ganin Erling Haaland ne ya kamata ya lashe Ballon d'Or na bana, bayan da ya ci Champions League da Premier League da FA Cup a Manchester City a bara.
Haka kuma tsohon dan wasan Borussia Dortmund ya ci kwallo 52 a wasa 53 a kakar da ta wuce.
Wasu da saka lashe kyautuka:
Haaland ya karbi kyautar Gerd Muller - kyauta ce saboda zun-zurutun kwallo 52 da ya zura a raga a wasa 53 a kakar da ta wuce.
Bellingham ya lashe kyautar Kopa Trophy - kyauta ce ta matashin da ba kamarsa a duniya a 2023.
Vinicius Jr ya karbi kyautar Socrates - Dan kasar Brazil ya samu wannan lambar yabon sakamakon gidauniyarsa ta taimakawa yara marasa gata a kasarsa.
Emiliano Martinez ya lashe kyautar Yashin - Tsohon wanda ya buga tamaula aro a Oxford United, shi ne gwarzon mai tsron raga a 2023.
Manchester City ce kungiyar kwallon kafa ta maza da ba kamarta a bara.
Kungiyar Etihad ta lashe kofin Champions League da Premier League da FA Cup a bara.
City tana da 'yan wasa bakwai daga 30 da suka yi takarar kyautar Ballon d'Or.
Kungiyar Barcelona ta mata ce kan gaba a bajinta a bana.
Ta lashe Champions League a bara da kofin Sifaniya - 'yan wasanta shida suna cikin takarar Ballon d'Or bangaren mata.