Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Kane na ci gaba da daga darajar Bayern Munich a Bundesliga
Harry Kane ya ci kwallo na tara a wasa na takwas a Bundesliga, bayan da Bayern Munich ta doke Mainz 3-1 a cikin ruwan sanyi ranar Asabar.
A minti na 11 da fara wasa ne Bayern ta zura kwallo a raga ta hannun Kingsley Coman, minti shida tsakani Harry Kane ya kara na biyu.
Kenan kwallo na tara da tsohon dan wasan Tottenham ya zura a raga da fara kakar bana.
Saura minti biyu da za su je hutu ne Mainz ta rage kwallo daya ta hannun Anthony Caci.
Sai dai bayan da suka koma zagaye na biyu ne, Leon Goretzka ya ci wa Bayern kwallo na uku a karawar ta mako na takwas.
Da wannan sakamakon Bayern tana mataki na uku a kan teburi da tazarar maki biyu tsakaninta da Bayer Leverkusen mai jan ragama da tazarar maki daya tsakaninta da Stuttgart ta biyu.
Leverkusen da Borussia Dortmund da kungiyar da Thomas Tuchel ke jan ragama, sune wadanda ba a ci ba a gasar Bundesliga kawo yanzu.
Bayern Munich tana mataki mai kyau da fara kakar bana, wadda take da maki biyar fiye da kwazon da ta yi a kakar da ta wuce a irin wannan matakin.
Kwazon da Kane ke yi a Jamus tun bayan da ya koma kungiyar daga Tottenham a bana, ya sa Bayern tana buga kaka mafi kwazo a karon farko tun bayan 2016-17.