Kofin Duniya na 2034 a Saudiyya: Abin da ya sa matakin bai zo da mamaki ba

An wallafa

Ƙarɓar baƙuncin gasar Kofin Duniya a Saudiyya, abu ne da aka jima ana burinsa, duba da yadda ƙasar ke zuba jari a fagen wasanni a shekarun baya-bayan nan.

To amma duk mutumin da ke la'akari kan yadda ƙasar ta gudanar da gagarumin sauye-sauye - a fannin wasannin ƙwallon golf ta hanyar shirya gasannin wasan, ko yadda ƙasar ta mamaye karɓar baƙuncin manyan gasannin damben zamani, ko kuma yadda ƙasar ta zuba jari a fagen kasuwancin 'yan wasan ƙallon ƙafa - hakan ba zai zama abin mamaki ba.

Yawan ganawa da shugaban Fifa, Gianni Infantino ke yi da Yariman Saudiyya a shekarun baya-bayan nan, ka iya zama wata alama ta yadda ƙasar ke ƙara zama mai ƙarfin faɗa-a-ji a fagen wasanni.

To amma, duk da matsayin ƙasar a fagen wasanni, batun ɗaukar nauyin gasar Kofin Dunya a Saudiyya zai bai wa mutane da dama mamaki.

A yanzu da ƙasar ke da kusan tabbacin damar ɗaukar nauyin gasar nan da shekara 11 masu zuwa, ƙasar za ta iya fuskantar ce-ce-ku-ce fiye da yadda Qatar ta fuskanta a shekarar da ta gabata.

Kama daga matsalolin da suka shafi tauye haƙƙin bil-adama, da yadda Fifa ke tafiyar da batun takarar daukar nauyin gasar, ga kuma batun sauya lokacin gasar, da kuma walwalar 'yan wasa sakamakon yiwuwar gudanar da gasar a lokacin hunturu, saboda matsancin zafi da ake fuskanta a lokacin bazara a ƙasar.

Ganin yadda aka faɗaɗa ƙasashen da za su halarci gasar zuwa 48, yawan sauye-sauyen da ƙasar za ta yi sun zarta na Qatar, sakamakon gina muhimman wuraren da ake buƙata, na ƙara saka shakku game da yadda ƙasar za ta tunkari wanna gagarumin sauyi.

Masu suka da dama na kallon hakan a matsayin nuna sha'awa a 'fagen wasanni' ga ƙasar da ke zama babbar mai fitar da man fetur a duniya.

Haka kuma akwai fargabar tauye haƙƙin mata, da haramta neman jinsi, da taƙaita 'yancin faɗar albarkacin baki, da ci gaba da yanke hukuncin kisa, ga batun zargin kisan fitaccen ɗan jaridar nan Jamal Khashoggi a 2018, tare da zargin hannun ƙasar a yaƙin Yemen.

To sai dai hukumomin Saudiyya sun sha musanta haka, suna masu cewa buƙatarsu ta ɗaukar nauyin gasar, zai taimaka wajen zamanantar da ƙasar, wajen inganta harkokin wasanni, tare da ƙarfafa wa matasa gwiwwa, bunƙasa yawon buɗe-ido, da bunƙansa hanyar samun kuɗin shiga ga ƙasar, kafin ƙarewar man fetur, tare kuma da haɗa kan ƙasashen duniya.

Sun nuna irin ci gaban da ƙasar ta samu a fagen ƙwallon ƙafar mata alal misali, suna masu cewa wannan wata dama ce ta ɓunƙasa harkokin wasannin ƙwallon ƙafa, bayan samun nasarar ɗaukar nauyin wasu gasanni.

Da ƙarfafa gasar ƙwallon ƙafar ƙasar ta 'Saudi Pro League' da sayen ƙungiyar Newcastle United, da kuma shirin ƙasar na ɗaukar nauyin gasar Kofin Duniya ta Ƙungiyoyi a lokacin hunturu, ga kuma ɗaukar nauyin gasar ƙasashen Asiya ta AFC a shekarar 2027.

To sai dai yayin da aka fi samun sha'awar ƙwallon ƙafa a Saudiyya fiye da Qatar, mutanen da ke halartar kallon gasar Pro League sun ragu a wanna kaka.

To amma ko ma mene ne manufar jagororin ƙasar, kasancewarta ƙasa ɗaya tilo da ke takarar karɓar baƙuncin gasar a 2034, zai rage wa Fifa wahalar yanke hukunci.

Sanarwar Fifa na gabatar da buƙatar karɓar baƙuncin gasar ta 2034 a farkon wannan wata ya zo wa mutane da ba-zata, kasancewar Fifa ta ƙayyade cewa dole ƙasar da za ta yi takarar ya fito daga yankin Asiya ko Oceania, tare da bayar da wa'adin kwana 26 ga masu takarar donsu bayyana sha'awarsu.

Daga nan - cikin 'yan mintuna - Saudiyya ta bayyana sha'awarta a hukumance, inda kuma hukumar ƙwallon ƙafar yankin Asiya ta nuna goyon bayanta kan matakin na Saudiyya.

A wani mataki kuma da wasu ke gani kamar alfarma aka yi wa Saudiyya, Fifa ta sasauta dokarta kan gina sabin filayen wasa, inda a yanzu ake buƙatar masu neman ɗaukar nauyin gasar su kasance suna da ginannu filayen wasa huɗu (a maimakon dokar yanzu ta filaye bakwai).

A yanzu da Australiya ta ɗauki matakin janyewa daga takarar, ana ganin ta yi hakan ne aboda ta san ba za ta iya ja da Saudiyya ba a wannan takara.

A watan Maris ne Ƙungiyar Shirya Gasannin Ƙwallon Ƙafa da Duniya - wadda ke wakiltar gasannin lig na ƙasashe a duniya - ta bayyana ''damuwarta" kan iƙirarin da ta yi na cewa Fifa ba ta tuntuɓeta ba kan sauya lokacin wasan ƙwallon ƙafa a duniya ciki har da ƙara yawan ƙasashen da za su halarci gasar Kofin Duniya ta 2026.

Haka kuma ƙungiyar kare haƙƙin bil-adama ta Human Rights Watch ta zargi Fifa da yin watsi da dokokinta, tana mai cewa "Abin kunya ne ga Fifa idan har ta bai wa Saudiyya damar ɗaukar nauyin gasar Kofin Duniya ta 2034, kasancewarta mai tarihin tauye haƙƙin bil-adama da rashin bayar da dama ga ƙungiyoyin kare haƙiƙin ɗa'adam don gudanar da ayyukansu, kuma tabbas hakan na saka shakku kan ƙudurin Fifa ta tabbatar da 'yancin ɗan'adam".

To sai dai Fifa ta ƙi cewa komai kan batun, to amma ta dage cewa 'yancin ɗan'adam na daga cikin manyan ƙa'idoji neman ɗaukar nauyin baƙuncin gasar.

Saudiyya za ta kasance ɗaya daga cikin ƙasashen da ɗaukar nauyin babbar gasar duniya ke janyo ce-ce-ku-ce a baya-bayan nan.

Alaƙar neman jinsi haramun ne a Morocco, wadda ke ɗaya daga cikin ƙasashen da za su karɓi baƙuncin gasar 2030, kamar yadda yake a Qatar, haka kuma batun yake a Saudiyya.

Maso goyon bayan auren jinsi, waɗanda suka ce ba sa jin za su samu kariya a gasar Kofin Duniyar da ya gabata, a yanzu za su ji ba lallai su halarci gasanni biyu masu zuwa ba.

Shin za a iya samun zanga-zangar 'yan wasa kamar yadda aka gani a Qatar, lokacin da tawagar Jamus ta nuna goyon bayanta ga masu neman jinsi?

Shin wasu ƙasashe za su ƙaurace wa gasar?

Abin da ke bayyane a fili shi ne yadda ake samun sauyi ta fuska wasanni a ƙasashen yankin Gabas ta Tsakiya.

A baya in aka ce ƙaramar ƙasa irin Qatar da maƙabciyarta Saudiyya za su iya ɗaukar nauyin baƙuncin gasar Kofin Duniya har guda biyu cikin shekara 12, mutane da dama za su yi mamakin hakan.

To amma idan aka yi la'akari da ɗimbin arzikin da ƙasashen ke da shi da yadda salon Fifa ya sauya musamman ƙarƙashin jagorancin shugabanta Gianni Infantino, hakan ba abin mamaki ba ne.

A yanzu 'yan ƙasar Saudiyya, za su ci gaba da kare kansu kan abin da suke gani a matsayin munafurci, suna nuni da hulɗar kasuwanci da mafi yawan ƙasashen Yamma ke jin ɗadin ƙullawa da su.

Suna masu cewa ƙasashen na jahiltar Saudiyya, kamar yadda tauraron damben boxing, Tyson Fury ya faɗa a baya-bayan nan, bayan ya yi wasa a birnin Riyadh, inda ya ce bai kamata mutane su yanke wa ƙasar hukunci kafin su ziyarce ta.

Hukumomin ƙasar za su kwatanta da Qatar, wadda duk kuwa da sukar da ta sha, ta samu damar ɗaukar nauyin gasar da mutane da dama suka kala a matsayin nasara.

Ko ma dai mene ne a yanzu Fifa da Hukumomin Saudiyya na da shekara 11 domin su nuna wa masu shakku cewa za su iya shirya gasar.