Nakan ji kunya idan matata ta wanke shimfiɗar da muka kwanta - Miji mai fitsarin kwance

An wallafa

Ga yara, yin fitsarin kwance ba wani sabon abu bane, amma idan babba ko wanda ya wuce shekaru 30 ya kasance yana yi fitsarin kwance, wannan lalura ce mai raɗaɗi da ake kira 'enuresis'.

Yawancin mutanen da ke fama da wannan cuta suna jin kunyar magana game da shi ko da kuwa akwai ƙwararru da suka amince da shi wanda su ka kware wajen neman hanyar magance matsalarsu. Amma enuresis matsala ce da za a iya gano ta cikin sauri, ko da an yi ƙoƙarin ɓoye ta.

"Ina jin kunya in kalli matata lokacin da take wanke shimfiɗar da muka kwanta da safe. Abin da ciwo," in ji Linus (ba sunansa na ainihi ba, ya nemi a sakaya sunansa), injiniyan kwamfuta mai shekaru 44 a Cotonou, Benin.

Mece ce lalurar fitsarin kwance 'enuresis'?

Lalurar fitsarin kwance 'Enuresis' shine yin fitsarin kwance ba da gangan ba yayin bacci. Wasu lalurace ta mafitsara wanda takan sa mutum ya kasa riƙe fitsari.

Ga yara 'yan ƙasa da shekara 5 ko 7, ba matsala ba ce a jika gado da fitsari koyaushe. Amma ga manya, hakan na iya haifar da wannan lalura kodayake yawancin mutane ba su san lalurar fitsarin kwance ba.

Da ƙyar ya iya bayyana wa BBC halin da yake ciki wanda a wasu lokuta yakan sa ya zauna a gida duk yini.

"Lalurar nan tana shafar dangantakata da mata ta, amma sa'a ta shine ina da mata mai fahimta wacce ke kula da ni sosai," in ji shi.

Wannan dama ce mai girma, kamar yadda ya bayyana, wanda ba ma'aurata da yawa ke da shi ba.

Irin wannan lalurar ta yi sanadin mutuwar aure da dama.

“Na fara jima’i musamman da daddare, bayan ‘yan watanni da aure da matata. “Ba zan iya bayyana ainihin abin da ke jawo hakan ba,” in ji shi, inda ya ƙara da cewa akwai damuwa a bangaren aikinsa domin yawan fitsarin da yake fama da shi ba shi da kyau, kuma a sakamakon haka ya kan shafe mafi yawan lokutan sa a gida.

Me ke janyo lalurar fitsarin kwance 'Enuresis'?

Yanayi na jiki da na tunani na iya haifar da lalular fitsarin kwance 'enuresis' ga manya.

Nau'in ciwon suga na 2 ko kamuwa da cutar yoyon fitsari na iya zama sanadin wannan lalurar, a cewar Dakta Anne-Marie.

Lalurar na iya faruwa sakamakon wani hatsari a cewar masana kamar irin rashin kulawa, yanayin mafarki da kuma shan taba na iya haifar da wannan lalurar..

Amma a cewar wani likita da ya ƙware a kan harkar mafitsara, lalurar fitsarin kwance na iya haifar da damuwa, da matsalar tsananin tunani, da tsoro ko rikicewa da kuma canjin a halayyar mutum.

Rage hulɗa da jama'a

Mutanen da ke fama da enuresis sau da yawa suna jin tsoro da kunyar magana akan lalurar tare da wasu, musamman ma waɗanda suke ƙaunarsu.

Kusanci da sauran mutane da tsoro na iya zama abubuwan da ke nisantar da su daga al'umma, kamar yadda Dakta Gaoussou ya bayyana yana cewa ya gamu da yawancin wadannan lulurori. Sau da yawa, lalurar fitsarin kwance ya kashe aure in ji likitan da ya ƙware a harkar mafitsara wanda ya ce akwai magunguna masu tasiri don shawo kan wannan batu lalurar fitsarin kwance.

Amma Linus, bisa ga kwarin gwiwarsa, babu wani abin damuwa a kan shi ma ba zai iya bayyana hakurin matarsa ​​da abin da ya kira mafi duhun lokutan rayuwarsa ba.

Dan uwansa dan wasan tennis wanda ya zama babban abokinsa a rayuwarsa na taimaka masa idan suka yi tafiye-tafiye ta hanyar kawo ƙunzugu don kada ya ji kunya a cikin al'umma.

Bugu da ƙari, ba ya fita waje, irin wurare kamar shaƙatawa da abokai ko zama tare da dangi.

Ya fi son zama a gida matarsa ​​ta kula da shi sosai. “Abin farin cikin shine yana da wahala luluarar za same ni da rana."

Ya kuma jaddada cewa magugunan da aka yi masa ya taimaka,” amma kuma ya ƙara da cewa: "Har yanzu dole ne in shawo kan lamarin a cikin dare."

Ana iya magance lalurar fitsarin kwance ga manya

Babu wani takaimaiman magani ga wannan lalurar na fitsarin kwance a cewar ƙwararun likitoci a harka mafitsara, yanayin rayuwa mai kyau na iya taimakawa wajen magance wannan lalurar.

Likitoci sun dage kan shawarwari kan yadda mutane za su gudanar da rayuwarsu domin magance wannan lalurar ta fitsarin kwance ga manya. Ya kamata manya su bi a hankali wajen shan ruwa ko wajen amfani da ruwa.

Kuma, ya kamata a guje wa shan kofi da abubuwan zaƙi. Suna taimakawa wajen motsa mafitsara kuma wani lokaci suna haifar da yawan fitsari.

Amma Linus ya ce yana da matuƙar wahala mutum ya daina abubuwan da ya saba kamar su shan kofi, da zaƙi yayin da yake mayar da martani kan shawarwarin likitoci domin warkar da lalurar fitsarin kwance.

Likita na kuma iya rubuta wasu magunguna idan irin shawarwarin nan ba su haifar da sakamako mai gamsarwa ba. Magani ne da ke taimakawa wajen tsayar da kwararar fitsari da daddare.

Amma maganin bai cika tasiri ba kamar da wasu". Har ila yau, wasu masana ilimi a harkar mafitsara sun ba da shawarar hada hanyoyin biyu na magani wanda ya haɗa da shawarwari da kuma magungunan sha domin samun sakamako mai kyau.

Wata hanyar da aka ba da shawarar domin magance lalurar fitsarin kwance shine motsa jikin da ake kira 'Kegel.'

Motsa jiki ne wanda ke nufin ƙarfafa tsokoki na ƙashin ƙugu kuma sau da yawa yana haifar da cikakkiyar farfadowa.

Lalurar fitsarin kwance 'Enuresis', a cewar masana da yawa, ana ɗaukarsa a matsayin "cuta d mutane ke jin kunyarsa" wanda ke sa yawancin masu fama da shi su samu sarawar gwiwa kuma su dinga janye wa daga cikin al'umma. Laluarar ya fi aukuwa ga mata fiye da maza.