Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Abin da ya kamata ku sani kan wasan Sociedad da Barca
Barcelona ta ziyarci Real Sociedad, domin karawa a wasan mako na 12 a gasar La Liga da za su kara ranar Asabar.
Kungiyar Camp Nou tana mataki na hudu a kan teburin La Liga da maki 24, ita kuwa Sosiedad mai maki 19 tana ta biyar.
Barcelona, wadda ta yi rashin nasara a karon farko a bana a El Clasico da Real ta doke ta 2-1, za ta kece raini da Sociedad, wadda wasa biyu ta yi rashin nasara.
Labari da ya shafi kungiyoyin biyu:
Yawancin 'yan wasan Barcelona da ke jinya sun murmure har wasu ma sun koma buga mata tamaula.
Robert Lewandowski da Raphinha sun buga wa Barca El Clasico, wadanda aka sa daga baya, yayin da Jules Kounde ya yi zaman benci.
Ranar Juma'a Barcelona ta sanar cewar Pedri ya murmure, yana cikin 'yan wasa 20 da ta je da shi gidan Sociedad.
Kenan Frenkie de Jong da Sergi Roberto ne kadai 'yan wasan Barca da suka rage masu jinya.
Ita kuwa Real Sociedad tana da 'yan wasa uku da ke jinya da suka hada da Mikel Merino da Ander Barrenetxea da kuma Igor Zubeldia.
Shin ko ka san?
Barcelona ba ta yi rashin nasara ba a karawa 12 baya da ta je Sociedad, wadda ta yi nasara tara da canjaras uku.
Koci, Xavi yana cikin 'yan wasan da Barcelona ta yi wadannan nasarorin a lokacin da ta dunga yi wa Sociedad fintinkau.
Haka kuma Xavi a matakinsa na koci ya ja ragamar zuwa Sociedad karo biyu yan doke ta, wanda ke fatan nasara karo na uku a jere.
Robert Lewandowski ya ci kwallo a dukkan wasa biyu da ya fuskanci Sociedad, wanda ke fatan yin bajinta ta uku a jere, kamar yadda ya yiwa Betis.