Ethan Nwaneri ya zama matashin da ya fara buga Premier

Asalin hoton, Getty Images
Mai shekara 15 da haihuwa, Ethan Nwaneri ya zama matashin da ya fara buga Premier League a wasan da Arsenal ta doke Brentford 3-0 ranar Lahadi.
Dan wasan tawagar Ingila, wanda aka haifa a cikin Maris din 2007, ya canji Fabio Vieira daf da za a tashi a filin Brentford Community.
Nwaneri mai shekara 15 da kwana 181 ya doke tarihin da Harvey Elliott ya kafa a baya.
Elliot dan wasan Liverpool ya kafa tarihin matashin da ya buga babbar gasar tamaula ta Ingila yana da shekara 16 da kwana 30 a wasa da Fulham a 2012.
Nwaneri ya canji Vieira a minti na 91 da dakika biyu, wato ya yi minti uku da dakika 42 a cikin fili da aka tashi wasan a minti na 94 da dakika 44.
Shi ne dan kwallo na farko da yake kasa da shekara 16 da ya fara taka leda a Premier League.
Nwaneri ya buga wa matasan Arsenal 'yan kasa da shekara 18 wasannin da yawa da tawagar Ingila ta 'yan shekara 16 tun yana da shekara 14 da haihuwa.











