Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Masu fafatawa da Bala Ƙaura a takarar gwamnan jihar Bauchi
Jihar Bauchi da ke yankin arewa maso gabashin Najeriya ta kasance ɗaya daga cikin jihohin da harkokin siyasarsu ke ɗaukar hankali a ƙasar.
Jiha ce da ke da tarihin fitattun 'yan siyasa a Najeriya tun daga jamhuriya ta farko har zuwa yau, domin kuwa ita ce jihar da ta samar da firaministan Najeriya na farko, Sir Abubakar Tafawa Ɓalewa.
Tun bayan komawar ƙasar kan tafarkin mulkin Dimokraɗiyya a shekarar 1999 an yi gwamnoni huɗu a jihar, wadda ake yi wa laƙabi da birnin Yakubu.
Tun daga kan Ahmad Adamu Mu'azu wanda ya kwashe shekarar takwas a kan karagar mulkin jihar, daga 1999 zuwa 2007, sai Malam Isa Yuguda daga 2007 zuwa 2015, da M.A Abubakar wanda ya yi mulkin shekara huɗu, wato 2015 zuwa 2019, sai kuma gwamna mai ci Bala Abdulƙadir Mohammed wanda a yanzu ke neman wa'adi na biyu.
A zaɓen da za a gudanar ranar 18 ga watan Maris akwai 'yan takara 13 da za su fafata domin neman ɗarewa kan kujerar gwamnan jihar.
Bala Abdulƙadir Mohammed - PDP
Sanata Bala Abdulƙadir Mohammed shi ne gwamnan jihar mai ci na jam'iyyar PDP, wanda ya fara mulkin jihar a shekarar 2019 lokacin da ya kayar da gwamna mai ci na wancan lokacin Baristar M.A Abubakar na jam'iyyar APC.
Sanata Bala Mohammed da ake yi wa laƙabi da Ƙauran Bauchi ya wakilci Bauchi ta kudu a majalisar dattawan Najeriya a 2007, inda ya kasance ɗaya daga cikin fitattun sanatoci a lokacin.
A shekarar 2010 tsohon shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ya naɗa shi ministan birnin tarayyar ƙasar, Abuja.
A shekarar 2019 ya tsaya takarar gwamnan jihar inda ya samu nasara a kan gwamnan jihar na lokacin, Mohammed Abdullahi Abubukar wanda ya nemi wa'adin mulki na biyu.
Abubakar Baba Sadique - APC
Toshon babban hafsan sojin sama na Najeriya shi ne ɗan takarar gwamnan jihar a jam'iyyar APC .
Kafin shigar sa harkokin siyasa a shekarar 2022 ya riƙe muƙamin babban hafsan sojin sama na Najeriya daga shekarar 2015 zuwa watan Janairun 2021, daga nan kuma shugaba Buhari ya naɗa shi a matsayin jakadan Najeriya a ƙasar Chadi.
Air Marshal Sadique Baba Abubakar mai ritaya ya kasance miji ga ministar ayyukan jin-ƙai ta ƙasar, Sadiya Umar Farouk, wadda ya aura a shekarar 2020.
Halliru Dauda Jika - NNPP
Sanata Halliru Dauda Jika, ɗan kasuwa kuma ɗan siyasa ya taɓa zama kakakin majalisar dokokin jihar Bauchi.
Sannan ya wakilci ƙananan hukumomin Darazo da Ganjuwa a majalisar wakilai ta tarayya har sau biyu, kafin ya zama sanata a yanzu da ke wakiltar Bauchi ta tsakiya, kuma shugaban kwamitin majalisar dattawa kan harkokin 'yan sanda.
Halliru Jika wanda aka fi sani da Dokaji shi ne ɗan takarar kujerar gwamnan Bauchi ƙarƙashin jam'iyyar NNPP.
End of Ƙarin labaran da za ku so ku karanta:
Umar Farouk Ahmed - PRP
Umar Farouk Ahmed, wanda ke da digiri na biyu a fannin shari'a, ya kwashe shekara 15 yana aikin lauya.
Tsohon mai taimaka wa shugaban majalisar dattawan Najeriya Sana Bukola Saraki ne a fannin shari'a.
Umar - wanda shi ne kuma tsohon shugaban hukumar bunƙasa mata da matasa ta jihar Bauchi - ya yi takarar mataimakin gwamnan jihar a shekarar 2019.
Shi ne ɗan takarar gwamnan Bauchi a jam'iyyar PRP.
Abukabar Ibrahim - LP
Tsohon manajan banki da ya kwashe tsawon shekara goma yana jagorantar bankin bayar da rance ga masu ƙananan sana'o'i na Garu.
Abubakar Ibrahim - wanda ke da shaidar karatu ta HND a ɓangaren akanta - ya kasance mamba a cibiyar horas da akantoci ta Najeriya.
Sauran 'yan takara da jam'iyyunsu
Musa Magaji - AA
Idris Buhari Adamu - AAC
Saleh Auwalu Dahiru - ADC
Usman Dankyarana Mustapha - ADP
Isah Auwal - APM
Kabiru Abdulhamid - APP
Saleh Sulaiman - NRM
Mohammed Aminu - SDP
Hassan khalid - ZLP