Saudiyya na son ɗaukar nauyin Kofin Duniya na mata 2035

An wallafa

Saudiyya na son ɗaukar nauyin gasar cin kofin duniya ta mata da za a yi a 2035, kamar yadda daraktan wasannin bangaren mata ta ƙasar ta bayyana.

Tuni Masarautar ta shigar da buƙatarta ta ɗaukar nauyin gasar kofin duniya na maza da za a yi a 2034.

"Ina da yaƙinin wasannin mata da 'yan mata na da goben da za ta haskaka a Saudiyya," in ji Monika Staab.

Ana zargin Saudiyya da take haƙƙin ɗan adam tun bayan haramta auren jinsi da yake cikin dokokinta.

Haka kuma ana nuna damuwa kan cewa mata ba su da cikakken 'yanci a ƙasar.

'Yan wasan kwallon kafa mata sun nuna damuwa kan jinsin da suke nema, yayin da aka riƙa suka kan shirin hukumar yawon buɗe ido ta saudiyya da ta nemi ɗaukar nauyin kofin duniya na 2023 da ya gudana a Australia da New Zealand.

Daga baya Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Duniya Fifa ta yi watsi da wannan shiri, bayan ƙasashen da suka ɗauki nauyi sun nuna rashin amincewa kan wannan tayi.

A 2022 ne aka kafa tawagar mata ta Saudiyya, kuma ya zuwa yanzu ba ta kai ga buga gasa ko ɗaya ba.

"Na shaida wa shugabannin wasanninmu cewa zai ɗauki tawagarmu ta je gasar kofin duniya. Kuma na san suna shirin ɗaukar nauyin kofin duniya na maza - me ya sa ba za a ɗauki nayin ta mata ba ta 2035?" in ji Staab.

"Yanzu muna da tawagar kamata ya yi mu fara tunkarar gasa muga ni."