Messi ba zai je wata ƙungiya aro ba koda an gama gasar Amurka

Lionel Messi

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa

Lionel Messi ba zai je buga wasannin aro a wata ƙungiyar ba idan an kammala gasar tamaula ta Amurka in ji Guillem Balague.

Ana ta alaƙanta kyaftin din Inter Miami, mai shekara 36 da cewar zai koma taka leda a Barcelona ko kuma gasar tamaula ta Saudia Arabia.

Inter Miami an fitar da ita daga karawar cike gurbi ranar Asabar, bayan da Cincinati ta doke ta 1-0, za kuma a kammala kakar bana ranar 21 ga watan Oktoba.

Kyaftin din Argentina, wanda ya lashe kofin duniya a Qatar a 2022 ya buga minti 72 a gasar Amurka cikin Satumba, yayin da ya yi fama da rauni.

Idan an kammala gasar kwallon kafa ta Amurka, MLS, Argentina za ta buga karawar neman shiga gasar cin kofin duniya da Uruguay ranar 17 ga watan Oktoba.

Haka kuma za ta yi karawar hamayya da Brazil a dai fafatawar neman shiga gasar kofin duniya ranar 22 ga watan Nuwamba daga nan ne Messi zai dauki hutun wata daya.

''Messi zai yi hutun wata daya kamar yadda kowanne dan kwallo ke yi. Saboda haka ba wata maganar zai koma Saudi Arabia'', in ji fitatcen mai sharhin tamaula Balague.

Daga nan zai koma buga karawar share fagen tunkarar kakar badi da Inter Miami don shirin fara kakar badi a watan Fabrairun 2024.

Mai rike da kyautar Ballon d'Or bakwai ya koma Inter Miami daga Paris St-Germain a watan Yuli, ya kuma ja ragamar kungiyar ta dauki kofin farko a tarihi, inda ta lashe Leagues Cup cikin Agusta daga nan ta yi nasara a kofin US Open.

An dade ana ta alakanta Messi da cewar zai koma tsohuwar ƙungiyarsa ta Barcelona tun bayan da ya koma PSG a 2021, bayan shekara 21 yana taka leda a Sifaniya.