Cinikin ƴan wasan da kwalliya ta biya kuɗin sabulu a watan Janairu

An wallafa

Tun daga 1 ga watan Janairu, aka buɗe kasuwar musayar ƴan ƙwallo a wasu ƙasahen Turai, kuma za ta ci gaba da kankama har zuwa ƙarshen watan.

To sai dai a irin wannan lokaci, gasar ƙasashen Turai ta yi nisa, har ta kai gangara, inda aka shiga zagaye na biyu a wasu wasannin.

Abin da ke nuni da cewa, da wuya wata ƙungiya ta sayar da wani fitaccen ɗan ƙwallonta a Janairu, domin lokacin tana fatan ƙara ƙarfi domin kammala kakar bana a mataki mai kyau.

Sai dai wasu lokuta, ƙungiyoyi kan iya sayar da zaƙaƙuran 'yan ƙwallonsu, don su samu kuɗin da za su sayo sabbin ƴan wasa, don ƙara ƙarfi.

Wasu kuma sukan sayar da fitattun ƴan wasa a watan Janairu, idan sun samu rashin jituwa da ɗan kwallo, ko kuma idan yana yawan tafiya rauni ko wanda ba ya kan ganiya.

A watan na Janairu a gasar Premier League, a baya can an yi cefanen da har kwalliya ta biya kuɗin sabulu ga ƙungiyoyi.

Ƴan wasan da aka saya a watan Janairu, sannan suka taka rawar gani sun hada da Nemanja Vidic da Luis Suarez da Andy Cole da Virgil van Dijk da Julian Alvarez da sauranssu.

Liverpool ta tuntuɓi Virgil van Dijk cikin sirri a 2017, daga baya batun ya fito fili, inda ta bai wa Southampton haƙuri.

Liverpool daga bisani ta bi ta hanyar da ta dace wajen zawarcin ɗan ƙwallon na ƙasar Netherlands - ranar 27 ga watan Disamba, Southampton ta sanar cewar ɗan ƙwallon zai koma Anfield, da zarar an buɗe kasuwa a watan Janairu.

Tun bayan komawarsa Anfield da taka leda, Van Dijk ya taimaka wa Liverpool har ta ɗauki Premier League a 2019/20, na farko bayan shekara 30.

Haka kuma mai shekara 32 ya lashe Champions League da FA Cup da EFL Cup da Uefa Super Cup da kuma Fifa Club World Cup duk a ƙungiyar ta Merseyside.

Nemanja Vidic

Bari mu koma 2006, inda Sir Alex Ferguson ya ce ''Fitattun 'yan baya na ba da gudunmawa wajen lashe kofuna'' bayan ya ɗauki ɗan ƙasar Serbia, Nemanja Vidic.

Kuma Ferguson bai yi kuskure ba a maganarsa, inda Vidic ya yi kaka takwas a Old Trafford da zama kyaftin a Manchester United.

Lokacin da Vidic ya taka leda a Manchester United, ya lashe Premier League biyar da League Cup uku da Champions League da kuma Fifa Club World Cup.

Seamus Coleman

Lokacin da Everton ta sanar da sayen ɗan wasa mai tsaron baya daga gefen hagu a gasar lik ɗin Ireland a kan £60,000 - ba wanda ya ɗauka Seamus Coleman zai zama ƙashin bayan ƙungiyar.

Mai shekara 35 ya yi fama da jinya daga ƙarshe, amma ya buga wasa 411 a dukkan karawa na ƙungiyar ta Goodison Park

Idan ka kwatanta kuɗinsa ya kai £146 a kowanne wasa.

Ko da yake a lokacin da ya taka leda a Everton, ba ta ɗauki kofi ba, amma an ci ribar cinikinsa, ya kuma taka rawar da ta dace a ƙungiyar ta Merseyside.