Liverpool ta yi waje da Arsenal daga FA Cup

An wallafa

Liverpool ta fitar da Arsenal daga FA Cup karawar zagaye na uku, bayan da ta ci 2-0 a Emirates ranar Lahadi.

Kenan ƙungiyar Anfield ta kai zagaye na huɗu, bayan da Jakub Kiwior ya ci gida da kuma Luis Diaz ya zura na biyu a raga .

Arsenal ta ɓarar da damar maki da yawa, wadda ta ƙasa zura kwallo a raga daga baya Liverpool ta amfana a bugun tazara da Kiwior ya ci gida saura minti bakwai a tashi wasan.

Daf da za a tashi daga karawar Diaz ya zura na biyu a raga da hakan ya kai Liverpool zagaye na huɗu a FA Cup.

Ƙungiyar da Mikel Arteta ke jan ragama ta buga kwallo ya bugi turke ta hannun Martin Odegaard, yayin da Reis Nelson da Kai Havertz suka kasa cin kwallo.

Liverpool, wadda ta buga karawar ba kyaftin Virgil van Dijk, wanda ya yi rashin lafiya ta yi ƙoƙarin ganin ta fitar da Arsenal har gida a wasan.

Mai tsaron raga, Aaron Ramsdale ya hana kwallon da Diaz ya buga ya shiga raga, yayin da Diogo Jota ya sa kai amma kwallo ya bugi turke.

Arsenal tana mataki na huɗu a teburin Premier League da maki 40 iri ɗaya da na Manchester City ta huɗu.

Liverpool ce ta ɗaya da maki 45, sai Aston Villa ta biyu mai maki 42 a teburin babbar gasar tamaula ta Ingila.