Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Mutum 20 sun mutu a gidan rawa a Afrika Ta Kudu
An gano gawar akalla mutum 20 a wani gidan rawa da ke birnin East London da ke kasar Afirka ta Kudu, a cewar jami'ai.
An gano gawarwakin ne a gidan rawar Enyobeni Tavern da safiyar Lahadi, kuma rahotanni sun ce mutane da dama sun jikkata.
"Ana gudanar da bincike kan yadda mutanen suka mutu a halin yanzu da nake magana da ku," a cewar kakakin rundunr 'yan sanda, a hirarsa da gidan talbijin na the Newzroom Africa television channel.
"Ba ma son yin hasashe kan abin da ya haddasa mutuwarsu a wannan matako," a cewar Birgediya Tembinkosi Kinana.
Ma'aikatan bayar da agajin gaggawa da dama sun hallara a wurin da lamarin ya faru da ke Lardin Gabashin Cape.
Rahotanni sun ce 'yan uwan mutanen da lamarin ya rutsa da su ba su iya ganin gawarwakin dangin nasu ba, sannan jama'a sun yi kira da a rufe gidan rawar.
Kwamishinan 'yan sandan Gabashin Cape Nomthetheleli Lilian Mene ya shaida wa kafar yada labarai ta SABC News cewa "an yi turmutsutsin da bai halasta ba a gidan rawar na tavern".
BBC ba ta tabbatar da wannan bayani ba kuma har yanzu babu cikakkun bayanai game da lamarin.
SABC ya rawaito cewa an kai mutum hudu asibiti.
Birgediya Kinana ya shaida wa manema labarai cewa akasarin mutanen da suka mutu matasa ne masu shekaru tsakanin 18 zuwa 20.
Ganau sun gaya wa jaridar Daily Dispatch cewa sun ga gawarwakin mutane a kwance cikin gidan rawar kamar sun fadi a dandarin kasa.